Wani bangare na allurar rigakafin COVID-19 na kamfanin Sinopharm da Sin ta bayar da gudummuwarta ga kasar Equatorial Guinea, ya isa Malabo, babban birnin kasar a jiya Laraba.
Yayin wani taron manema labarai a jiya, kakakin ma’aikatar harkokin wajen Sin, Wang Wenbin, ya ce wannan shi ne kashin farko na tallafin alluran rigakafi da gwamnatin Sin ta samar ga kasashen Afrika.
Da yake karbar rigakafin a filin jirgin saman Malabo, mataimakin shugaban kasar Teodoro Nguema Obiang Mangue, ya ce tallafin alama ce ta kyakkyawar dangantakar dake tsakanin kasashen biyu.
A nata bangaren, jakadiyar Sin a Equatorial Guinea, Qi Mei, ta ce yayin taron Sin da Afrika kan hadin gwiwar yaki da COVID-19 da ya gudana a watan Yunin 2020, Sin ta ba kasashen Afrika tabbacin kasancewa na farko da za su ci gajiyar alluran rigakafin kasar, kuma a yanzu, Sin din ta cika alkawarinta na bayar da rigakafin ga Equatorial Guinea, wanda zai taimaka mata cin galaba a kan cutar.
Ta kara da cewa, kasashen duniya sun yarda da nagarta da amincin alluran rigakafin na Sin. Ta ce duk da dimbin bukatar allurar da ake da ita a cikin kasar, Sin ta kuduri niyyar shawo kan kalubalen samar da ita kan farashi mai rahusa ga kasashe masu tasowa. (Mai fassarawa: Fa’iza Mustapha daga CRI Hausa)