Connect with us

Uncategorized

Gudunmawar Kungiyoyi Wajen Samar Da Zaman Lafiya Da Fahimta (2)

Published

on

Saboda muhimmancin abubuwan da suka shafi zaman lafiya da fahimtar juna, ya sa a yau ma za mu kawo maku wannan bayani na irin da gudumawar da gidauniyar UFUK DIALOGUE ke bayarwa, musamman wajen bangaren samar da zaman lafiya da fahimtar juna, inda muke tabo irin gudumawar da take bayarwa a wannan fanni, ta hanyoyin gudanar da taruka.
Na kuma bayyana mana cewa wannan gidauniya tana gudanar da ayyuka da dama a wannan kasa, ciki kuwa har da gudanar da tarukan samar da fahimtar juna a tsakanin jama’a, inda ake tattara mutane masu mabambantan ra’ayoyi ana musayar ra’ayi domin amfanin juna wajen samar da fahimtar juna da zaman lafiya.
A makonnin da suka gabata na bayyana cewa a wasu kwanaki can, UFUK DIALOGUE ta gudanar da irin wannan taro a garuruwan Abuja, Legos da Kaduna, inda suka samu hadin gwiwa da wasu Hukumomin kasar nan wajen gudanar da tarukan. Kamar yadda na kawo a makon da ya gabata, akwai IPCR, ECOWAS, NDA, NCWS, Ma’aikatar yada labarai da al’adu, ma’aikatar matasa da wasanni da kuma jaridar DAILY TRUST.
Za mu dan maimaita wasu bayanai kadan don amfanin wadanda ba su samu ganin jaridarmu da ta gabata ba, wanda kuma yana da matukar muhimmanci a ji wadannan bayanai.
Ga wanda bai san wannan kungiya ba, a takaice za mu iya cewa ita Gidauniyar UFUK DIALOGUE ta Sasantawa ce a tsakanin addinai da al’adu, wacce wasu mutanen kasar Turkiyya, almajiran Shaihin Malamin nan, Fethullah Gulen suka kirkiro a kasar nan. Manufa da ayyukansu, ne shirya dandali da tarukkan sasantawa da kaunar juna da yafiya da cudanyar juna a tsakanin mabambantan addinai da ala’adu domin samun ci gaba mai dorewa.
Gidauniyar ta UFUK DIALOGUE ta shirya taron shekarar 2018 ne, mai taken Soyayya Da Hakuri Da Juna, watau lobe and tolerance, wanda shi ne na hudu a jerin sahun tarrurkan da ta ke shirya, wanda n ace sun gudanar a Abuja Legas da Kaduna.
A Kaduna, taron ya gudana ne a a Gidan Hassa Usman Katsina da ke Kan hanyar Kawo a Kaduna, inda mahalarta taron sun tattaro kowane sashe na al’umma ,kama daga Malaman addinan Musulunci da Kiristanci da ‘yan kasuwa da jami’an tsaro da jama’an gwamnati da dalibai da ‘yan jarida da Sarakunan gargajiya da sauransu.
A Jawabinsa na maraba da baki, Shugaban Gidauniyar ta UFUK DIALOGUE, Mista Kamil Kemanci ya bayyana Gidauniyar a takaice da kuma ayyukanta tun lokacin da aka kafa ta a shekarar 2011 a kasar nan. Mista Kemanci ya ce tarurruka irin wadannan ba abin wasa ba ne, idan aka yi la’akari da irin yadda rashin jituwa da tashe-tashen hakula, ko rikice-rikice ke faruwa a ciikin al’ummar duniya, ba ma na Nijeriya kadai ba.
Ya kuma bayyana fahimta da akidun Shaihun Malaminsu Fethullah Gulen, wanda ya kaurace wa duniya yana bautar Allah da kuma koyar da zaman lafiya da ilmi a cikin al’umma.
Da yake magana a wajen taron, Gwamna jihar Kaduna, Malam Nasiru El-rufai, wanda mataimakinsa, Barnabas Bala Banted ya wakilta, ya jawo hankalin ‘yan Najriya akan muhimmancin zaman lafiya da kawar da bambance-bambancen da ke tsakaninsu, inda ya yi magana mai tsawo akan rikcin Fulani da makiyaya.
Ya ce tilas ne a cire maganar addini da kabilanci a wannan rikicin, a kalle shi ta fuskar tattalin arzikin kasa, da kuma gano mafita, wacce za ta amfani Fulanin da sauran al’ummar kasar nan. “Tun ina dan majalisar tarayya na taba kawo wannan batun na rikicin makiyaya da manoma, amma sai sauran ‘yan majalisun ba su dabi batun da wani muhimmanci ba, sai ga shi abin da ba a son shi ne yake faruwa a halin yanzu,” in ji Mataimakin Gwamnan.
Ya kara da cewa, “abin takaici ne wasu sun sanya maganar addini da kabilanci a al’amarin, maimakon a kalle shi ta fuskantar matsalar tattalin arzikin kasa.”
A nasa jawabin, mai magana na farko, Sakataren kungiyarJama’atu Nasril Islam, Dokta Khalid Abubakar ya ce idan ana son a samu zaman lafiya sai an samu soyayyar juna da hakuri da juna mai dorewa a cikin al’umma. Ya kawo koyarwar Fethullah Gulen, inda ya ce soyayyar wani babban al’amari ce a zamantakewar dan adama, sannan tausayi da rahma da yafiya da kuma juriya da juna.
Dokta Khalid ya ce sasantawa ita ce a cire ganin girman kai da amince wa gaskiya ta bayyana, ba tare da son zuciya ba, inda ya kawo ayoyin Alkurani mai tsarki domin ya tabbatar da hujjojinsa. Daga nan ya kawo rabe-rabe da tsattsauran akidoji da illolinsu a cikin al’umma, da kuma hanyoyin da za a bi domin magance su gaba daya.
Hanyoyin, in ji shi, sun hada gano al’ummun da talauci ya yi wa kanta ko wadanda aka zalunta suna son su yi ramuwar gayya, samar da Malamai masu hikimar magana da iya jawo hankali wadanda za su lallami al’ummar da ka iya fadawa cikin tsattsauran ra’ayi ko wadanda aka zalunta da samar da jagoranci na adalci da gaskiya ba tare da nuna bambanci ba.
A mukalar da ya gabatar a wurin taron, Dokta A.O. Yahaya na sashen Akawu na Jami’ar Horos da Sojoji ta kasa, NDA Kaduna mai suna ‘Yadda za a magance tsauraran ra’ayoyi a cikin al’umma,’ ya hakikance cewa, iyali su ne kashin bayan magance tsauraran ra’ayoyi a cikin al’umma, inda ya kawo misalai da dama domin ya tabbatar da ikirarinsa.
Muna fata za a samu irin wadannan kungiyoyi, ko gidauniyoyi, wadanda za su shiga gaba wajen ganin al’umma ta samu fahimtar juna a tsakaninsu, musamman ta nahyar shira tarurrukan kara wa juna sani da kusan tar juna, kamar irin wannan da UFUK ke gabatarwa.
Domin a hakikanin gaskya irin wannnan abu, ana ganinsa kamar ba komai, zai iya bayar da gagarumar gudumawa wajen samar da fahimtar juna a tsakanin jama’a, domin sai da fahimtar juna ne ake samun cikakken zaman lafiya.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: