Connect with us

TATTAUNAWA

Gudunmuwar Da Malama Tallu Dakingari Ta Bayar Ga Samu Da Ilimin Wasu Manyan Kasar Nan  

Published

on

LEADERSHIP A Yau Lahadi ta samu zakulu wata malama da ta bada  gudumuwar ta  ga ilmantar da wasu manyan kasar nan  maisuna Malama  Tallu Umar Dakingari  ‘yar shekaru 98 da haihuwa a Duniya da ke a karamar hukumar mulki ta Suru a jihar Kebbi.

Malama Tallu  Umar Dakingari ta shiga makarantar firamare a shekara ta 1942 a garin Dakingari da ake kira (Elementary school) a karkashen( Natibe Authority)wanda ta ce “ a lokacin da aka sani makaranta ina da shekara 6 da haihuwa a duniya haka kuma mata goma sha biyu ne kawai ake dauka a kowane aji ga lokacin domin turawa ne “. Hakazalika  a duk lokacin da aka koya muna lisafi da sauran wasu darussa  ni ce ke zama ta daya har ga lokacin mazan ajinmu suka fara cewar aljannu ke bani amsa saboda kokarin da Allah ya bani ga  lokacin.

Acewar malama Tallu Umar Dakingari  a cikin ‘yan ajinsu tasan akwai Arzika Daud, Baban tsohon akanta janar na jihar kebbi wanda na karantar da shi tsohon akanta janar wato Muhammad Arzika Dan-Atto, haka kuma akwai Atta Makeri sai kuma dukkan matan da nayi karatu tare dasu duk sun zanbabu wato sun mutu. Na kammala karatun firamare a shekara ta 1946 domin ga lokacin mu shekara hudu ake kammala karatun firamare, amma saboda zana karama sai da na shekara shidda kafin na wuce zuwa makarantar sakandare ta ‘yan mata wanda ake kira (Women Teachers College) a 1948 da ke sakkwato inda ta kammala karatun ta  a shekara ta 1953 a jihar ta sakkwaton.

Wanda a lokacin da muna WTC a jihar sakkwato duk dalibai sai an koya musu sana’ar hannu na dunki amma da hannu ba da keken dunki ba . A 1954 sai aka dauke mu aikin karantasuwa bayan na dawo Birnin-Kebbi ga lokacin mu hudu ne , amma kuma an bamu zabi na abin da kowane mu zai yi aiki akai ko aikin karantasuwa ko kuma aikin asibiti wanda mace daya daga cikinmu ta zabi aikin asibiti sai mu uku aka dauke mu aikin karantarwa inda aka tura  ni garin Dakingari wannan makarantar da nayi karatu a cikin ta wato (Elementary school) a matsayar malama . Bayan ta kwashe shekaru uku tana karantarwa sai aka canza ta zuwa  makarantar Nizamiyya a cikin garin na Dakingari inda ta ci gaba da aikin ta na malanta.

Har ilayau bayan ta koma share wasu shekuaru uku sai aka kara mata mukami zuwa matsayar shugabar makarata wato (HEADMASTER) . ta ce “ na iya aikin koyarwa a makarantun firamare a Dakingari har tsawon shekaru 33 kafin nayi ritaya daga aikin karantarwa a shekara ta 1987. Wanda a halin yanzu ina karbar Naira dubu Biyar a matsayar kudin fansho, inji malama Tallu Dakingari”. Haka kuma ina da yara guda tara wanda suma sun yi karatu har akwai masu digiri na farko har zuwa naBiyu,  bayan haka kuma daya daga cikin yara na akwai sojan ruwa wanda babba ne a cikin aikin . Hazalika ina da jikoki 64 wanda a cikin su akwai wadanda suka yi karatu har zuwa mataki na Dakta.

Malama Tallu yayin da ta koyar a matsayar ta ta malamar makaratar firamare  ta koyar da wasu dalibai da suka zama daya daga cikin manyan kasar nan wanda akwai Dakta, farfesa, sojoji da kuma jami’an ‘yan sanda da dai sauransu daga cikin daliban nata akwai  tsohon Gwamnan jihar Kebbi Saidu Usman Dakingari, Mainasara Saje tsohon Babban Sakatare a fadar gwamnatin jihar Kebbi, Manuga mil-guda, farfesa Umar Tuni, Dakta  Nura Rigistara na jami’ar Usmanu Danfodiyo da ke jihar sakkwato da kuma Hadiza mairukuta tsohonwar Rigistara a jami’ar gwamnatin jihar kebbi da ke Aliero.

Sauran sun hada da Hajiya Asama’u Kigo Dakingari matar Saidu tsohon Gwamna a jihar kebbi,Abdullahi Mai-Gari tsohon kwamishina a jihar kebbi, Hajiya Sidik  tsohon kwamishinan kiyon lafiya na jihar kebbi kuma yanzu shi ne Uban kasar Aljannare, sai Alhaji Jafaru Haliru Lamidon Dakingari  da kuma Alhaji Abdullahi Uban kasar Barbarejo da kuma sauran ire-irensu wanda wasun su na rike da manyan mukamai a  Abuja wanda bana iya tuna sunayensu, amma wadanda na bayyana sunayensu sun sansu.

Ganin irin yadda malama Tallu Umar ta sadaukar da kanta wurin koyar da dalibai a makarantun firamare na garin Dakingari, karamar hukumar mulki ta Suru a jihar kebbi wakilin LEADERSHIP Ayaulahadi yayi tattaki zuwa garin na Dakingari don  jin ta bakin ta kan yadda ake koyarwa a makarantun Boko a jahohin kasar nan ga kuma abin da  ta ke cewa” gaskiya yanzu ba a daukar kwararun malamai saboda kashe makarantun horas da malamai da aka yi tun farko domin a lokacinmu sai da muka yi karatu a makaratar koyon aikin malanta wato women teachers college kafin aka dauke mu aikin karantarwa, amma yanzu duk wanda ke da wata gata kawai sai kaga an bashi aikin karantarwa wanda baya bisa tsarin karantarwa,inji ta”.

Saboda haka  ina bada shawara ga gwamnatotin jahohin kasar nan da kuma hukumomin da abin ya shafa suyi gyara ga tsarin karantawa da kuma yadda ake daukar malamai a wannan karni.

Bugu da kari ta bukaci a yi bitar albashin malamai da kuma samar da kayan aikin ga malamai da kuma basu horo da haras suwa ta sanin makamar aikin karantarwa domin da akwai teachers colleges da duk wannan matsalar zata zo da sauki.

Ta ci gaba ta cewar “ idan gwamnatotin jahohi na da niyar gyaran harakokin ilimi tau su nemi tsofafin malaman makarantun firamare da kuma na sakandare  da suka yi karatun suna sakandare a teachers colleges domin suke da ilimin koyarwa wanda ake kira a turance (Grade two teacher) domin gaskiya yaran da ake dauka koyar a makarantu yanzu walahi basu san komi ba, inji malama Tallu Dakingari”.

Daga nan ta ya bawa daliban ta na 1984 kan shirya bikin karramawa da suka yimata a shekarun baya, wanda sune kawai suka tuna da cewa na koyar dasu a matsayata ta malamarsu a firamarai. Daga karshe ina kira ga uwaye da su tabbatar da sun baiwa yaransu    da kuma basu  ilimi mai ingance domin samun rayuwa mai kyau a zaman duniya da kuma lahira.
Advertisement

labarai