Gugar Zanan Buba Marwa Ga Atiku: Buhari Ya Kama Fadar Aso Rock, Sai Dai Ka Jira 2023

Tsohon Gwamnan Jihar Legas, Janar Buba Marwa (mai ritaya), ya sanar da duk masu hankoron ganin sun shiga fadar Aso, a matsayin shugabannin kasar nan cikin wannan shekarar ta 2019, da su janye wannan hankoron na su, domin kuwa a cewar sa, Shugaba Buhari ya rigaya ya kama kujerar ta fadar Aso, sai dai kuma duk mai kwadayin shiga Fadar ya tarba a shekarar 2023.
A cewar Buba Marwa, tuni al’umman kasar nan suka amince wa Shugaba Buhari da ya ci gaba da zama a wannan Fadar ta Aso, ya ci gaba da jan ragamar mulkin kasar nan domin tabbatar da dorewar ayyukan alherin da ya faro, gami da aiwatar da wadanda ya sa aniyar aiwatarwa ‘yan Nijeriya domin kawo gyara da maido da martabar kasar nan ta kowace fuska.
Buba Marwa, ya lissafo nasarori masu yawa wadanda gwamnatin ta Buhari ta samu a halin yanzu, a sassan da suka hada da nasarar da gwamnatin ta Buhari ta samu a sashen tsaro, Noma, yaki da cin hanci da rashawa, farfadowa da bunkasa tattalin arzikin kasa, samar da ayyukan yi, kokarin wadata kasar nan da hasken lantarki da sauran sassan kyautata rayuwar al’umman kasar nan.
Janar Marwa, wanda shi ne shugaban Kwamitin da Shugaban kasa ya kafa kan lalubo hanyoyin magance matsalar shaye-shayen muggan kwayoyi, ya yi wannan tsokacin ne a filin sauka da tashin Jiragen sama na Yola, a lokacin da yake amsa tambayoyi daga manema labarai jim kadan da tashinsa daga filin Jirgin saman a bayan ziyarar aiki na hukumar na shi da ya kai a Jihar ta Adamawa.
Janar Marwa, ya kara da cewa, “Ina da tabbacin duk wani da ya shiga wannan takarar da Shugaba Buhari a zaben na 2019, tabbas zai ci kasa ba tare da tantama ba.”
“Kungiyar Buba Marwa, ce ta farko da ta shirya gangamin nuna goyon baya ga Shugaba Buhari, tun a shekarar 2016, a bisa irin kyawawan ayyukan da Shugaba Buhari din yake aiwatarwa a sassan bunkasa tattalin arziki, tsaro da yaki da cin hanci da karban rashawa,” in ji Janar Marwa.
“Da izinin Allah, zai sake dawowa a karo na biyu; a kan haka, nake bayar da tabbaci ba tare da shakka ba, ga daukacin masu hankoron kujerar shugabancin kasar nan da su janye don gujewa shan kunya, su jira har sai a shekarar 2023,” in ji Buba Marwa.

Exit mobile version