Muazu Hardawa" />

Guguwa: Me Ya Sa Har Yanzu Gwamnati Ba Ta Waiwayi Mutane A Bauchi Ba?

Kimanin watanni uku kenan sama da gidaje dubu goma suka samu illa wacce ta shafi rushewar garu ko kwashewar rufi karama ko babba ko kuma rushewar gidan baki daya. Lamarin ya shafi gine ginen gwamnati da na talakawa da masu kudi da sauran jama’a inda kusan wannan ta’adi na iska da ya auku washegarin sallah  idan bai shafi mutum ba ya shafi na kusa da shi yadda kowane sashe na garin Bauchi da kewaye har kananan hukumomi sun samu lahani.

A gefe guda kuma sama da mutane 70 wannan matsala ta shafa yadda suka rasa rayukan su a cikin garin Bauchi da kewaye abin ya kasance kusan gidan kowa akwai matsala ko ta rauni ko rasa rai ko lalacewar gini ko kuma faduwar gini kan dukiya da ta shafi abin hawa ko dabbobi da makamantan su. Wannan abu yasa mutane sun yi ta kokawa yadda idan ka shiga wasu kauyuka da unguwannin talalkawa ‘yan rabbana ka wadata mu haka za ka samu ko ina cikin matsala. Wasu mutanen kuma sun kasance gidajen su sun rugurguje ga damina haka suka yi ta maleji a zauren makobta ko dangi, wasu kuma abin tausayi suka yi gidan leda da makamantan su don tsugunawa.

Wannan lamari ya kasance abin a tausayawa mutane kamar yadda gwamnatocin baya suke yi wajen ganin sun nemo tallafi daga aljihun gwamnati idan bala’i ya abku don rabawa mutanen da suka shiga matsala, kama daga kudi ko kayan abinci da na bukatun yau da kullum ko kayan gini da makamantan su.

Hakan ya sa mutane suka kasance da kyakykyawar fatar samun taimako daga gwamnatin Jiha da gwamnatin tarayya don a tallafawa mutane su fita daga mawuyacin halin da suka shiga musamman ganin yadda ake yin zato mai kyau wa gwamnatin tarayya karkashin jagorancin shugaba Muhammadu Buhari, da kuma gwamnan jihar Bauchi Mohammed Abdullahi Abubakar saboda tunanin gwamnatin su za ta ji tausayin talakawa kamar yadda a kullum suke ikirarin chanji na alheri wanda zai taimaki mutane su fita da cikin mawuyacin halin da suke cewa gwamnatocin siyasar baya da na soja duk azzalumai ne sun karya kasa sun talauta kasa sun sace kudin kasa. Don haka yanzu su ke sa himma neman kudi su taimakawa mutane don su san an samu gwamnati ta gaskiya.

Saboda haka tun daga lokacin da wannan masifa ta abko Jihar Bauchi tunanin kowa shine nan take za a samu tallafi mai yawa da mutane za su shaida wajen ganin ko ba a basu abin da za su gina gidajen su ba za a ba su tallafin da za su rage hanya ko rufe gidajen su yi ko kuma mai daki uku ya gyara daya ko biyu. Don haka mutane suka sakankance da jiran tallafin gwamnati kamar yadda aka saba gani, musamman ganin a lokacin gwamnan Jiha ya gayyato shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kawo ziyara Jihar Bauchi domin jajantawa mutane game da abin da faru. Shugaba Buhari ya sauka a jirgi mai saukar ungulu a makarantar horas da jami’an tsaro na ciki inda ya fito a mota ya shigo gari ya kai ziyara wa mai marataba sarkin Bauchi Alhaji Dokta Rilwanu Sulaimanu Adamu ya kuma kai ziyara gidan gwamnati ya gana da gwamna Mohammed Abdullahi Abubakar. Daga nan an zaci zai zaga zuwa ko daya daga cikin unguwannin da wannan matsala ta auku ya gani ya jajantawa mutane, amma ko kusa yana fita kurum sai ya nufi filin jirgin sama ya tashi ya koma inda ya fito. Bayan haka mutane sun ga musamman shugaban kasa ya ziyarci Bauchi kan wannan batu na ta’adin ruwa da iska kowa sai ya saki baki da tsammanin samun taimako ba tare da bata lokaci ba. Amma sai aka ji shiru har yau ba labari kimanin watanni uku, alhali lamarin ya faru bayan kowa ya yi hidimar sallah da abin da ya mallaka ba kudi a hannun sa balle ya gyara muhallin sa.

Ni na sani ko rantsuwa na yi ba zan yi kaffara ba, zai yi wahala a ce irin wannan ta’adi ya auku a Jihar Filato ko Binuwai ko Fatakwal ace ya tafi a banza ba tare da wani tallafin gaggawa ba daga  gwamnati kamar yadda aka yi biris  a Jihar Bauchi. Don haka duk maganar da ake yi na cewa Jihar Bauchi Jihar Baba Buhari ne wannan ba gaskiya bane don an ce ruwan da ya doke ka shine ruwa. Don haka mutanen wannan jiha babu abin da suka gani har zuwa wannan lokacin. Kuma wani abin kunya hatta tallafin da wasu mutanen irin su gwamna Ibrahim Hassan Dan Kwambo na Gombe da tsohon mataimakin shugaban kasa Alhaji Atiku Abubakar da sauran mutane irin su Mai Kanti Baru shugaban NNPC suka kawo har yau babu abin da aka bayar don rabawa wadannan mutane.

Idan an je hukumar bayar da agajin gaggawa ta Jihar Bauchi an tambaya har yanzu babu wani taimako sai ace akwai kayan abinci da wasu kayan bukata da gwamnatin tarayya ta kawo amma har yau ba a raba su ba. Idan an caccaki gwamna Mohammed Abdullahi Abubakar cewa har yanzu mutane basu ga wani taimako a kasa ba sai yace akwai kudi suna nan ana jira ne sai an samu kari a raba kudin. Kai wasu mutane da wannan bala’i ya shafa har sun mutu basu samu wani tallafi ba.

Kuma abin kunya shine yadda aka rika rabawa mutane mudu daya daya na masara ko na shinkafa ko garin kwaki,  wanda gidansa ya rushe me zai yi da mudu daya ko mudu biyu. Idan an yi magana kuma su ce wannan taimakon gwamna ne alhali a gefe guda wani dan siyasa sai ya kwashe buhuna ya kai gidan sa saboda zalunci. Batun ya zamanto tamkar an yi wa Jihar Bauchi baki yadda aka yi ko in kula da halin da talakawa masoya Buhari suka shiga. Kuma wani abin takaici an yi matsala a Jos da wasu sassa na kudancin kasar nan amma an kai musu tallafi, a Jihar Bauchi kuma batun ya zamo har ana shirin mancewa da wannan masifa da ta auku wannan ba karamin zalunci bane.

Wani abin takaici da muke samun labari shine kudin tallafi da aka tura zuwa Azare inda su kuma gobara ta kone shaguna masu yawa bayan an raba kudin sai aka ce gwamna ya tura a kawo kudin don ya samar da wasu a hada a raba, sai aka ce masa dama mutane a matse suke saboda sai sun fita su nemi abin da za su ci, don haka duk abin da aka samu an raba shi ga jama’ar da wannan bala’i ya shafa, kuma duk da wannan magana da ke yawo ba wanda ya fito ya musanta daga gwamnati.

A gefe guda kuma tun ana zargi da cewa ba wani taimako da ya zo, kuma wanda aka samu gwamnati ta rike ta gaza rabawa, har ana ganin kamar irin wannan kudin tallafi yana hannun sarkin Bauchi, don haka Sarki Rilwanu ya kira taron manema labarai ya wanke kansa da cewa dukkan kudi da kayan tallafi da aka kawo ya hannata su ga shugabannin kwamitin raba kayan da aka samar don haka shi babu komai a hannunsa kafin mutane suka wanke shi daga zargin da ake yi masa.

A gefe guda kuma idan an kira shugabannin kwamitin bincike game da abin da ya faru don a taimaka wanda gwamnati ta kafa sai su ce ba komai a hannun su, hatta man da suke zubawa a motoci suke zaga wajen da wannan abu ya auku a aljifansu suke zubawa, daga karshe idan an tambaye su basa iya magana sai su ce su ba abin da za su ce, lamari ya zamanto kamar wasan yara kuma a daidai lokacin da suke tsammanin za a sake fitowa a zabe su a matsayin shugabanni yadda suke ganin kamar abin da aka yi na gaza tallafawa ba cin amanar talakawa bane, yanzu za a sake basu goyon baya.

Hatta gine ginen gwamnati da suka lalace a Jihar Bauchi gwamna Mohammed Abdullahi Abubakar ya kasa gyarawa da wanda suke cikin fadar Jihar da wanda suke waje kamar yadda ake ganin wani sashe na ma’aikatar lafiya ta Jihar Bauchi da wannan iska ta lalata.  Lamarin da ke ba mutane mamaki tunda ginin gwamnati an kasa gyarawa yaushe talaka zai tsammaci za a tallafa masa ya gyara nasa ginin.

Don haka akwai aiki ja a Jihar Bauchi tun daga kan shugaban kasa Muhammadu Buhari da gwamna Mohammed Abdullahi Abubakar ba wanda ke tausayin talaka game da wannan bala’i da ya abka musu. Kuma na san idan da a ce a kudanci wannan abu ya faru dan arewa na shugabanci bai isa ace yau watanni uku kenan babu wani tallafi na a zo a gani ba, don haka ya ragewa mutane su fahimci masu kaunar su ko ku kuma masu cutar su, idan zabe ya zo su san yadda suma za su dauki fansa kan shugabanni marasa cika alkawari.

 

Exit mobile version