Guguwar Buhari Har Da Kara Da Kiyashi Ta Kwasa —Agwara

Daga Muhammad Awwal Umar, Minna

An yi kira ga matasan kasar nan da kar su yarda su sake maimaita kuskuren da suka tabka a zaben 2015 wanda hakan ne ya assasa durkushewar tattalin arzikin kasar nan. Dan majalisar dokokin jihar Neja mai wakiltar karamar hukumar Agwara, kuma shugaban marasa rinjaye a majalisar, Hon. Bello Ahmed ne yayi kiran a lokacin da yake zantawa da manema labarai a harabar majalisar dokokin.

Hon. Bello Ahmed ya ce yau abin kunya shugabannin mu ne ke tufka suna warwarewa, ya ce lokacin da maigirma gwamna ya rusa majalisar kwamishinoninsa shi da kan shi ne ya bayyana cewar ya rusa su ne saboda rashin tabuka komai, amma abin mamaki yau ya dawo da kashi tamanin cikin dari na rusassun a matsayin sabbin kwamishinonin da za a tantance dan mayar da su kan kujerar ta kwamishina wanda wannan kuskure ne a siyasan ce. Mu a matakin majalisa ba mu da ikon hanawa illa aikin da doka ya bamu na tsayar da su dan tantancewa kuma yanzu aikin da mu ke akai ke nan, dan haka kuskure ne, domin duk mutumin da ya kwana ya tashi zai saka alamar tambaya akan haka,  shugaba ya bata abu kuma ya dawo ya neman gyara shi wannan kuskure ne a siyasan ce.

Ya kamata idan za a yi zaben 2019 jama’a su zura idanunsu dan zabo nagartattun mutane da zasu shugabancin su, a matakai na shugabanci a kasar nan.

Dan majalisar ya ce a halin da ake ciki talaka na cikin matsin lamba saboda tabarbarewar tattalin arzikin kasa, ma’aikacin gwamnati na kuka, dan kasuwa na kuka, yace bayan tabarbarewar tattalin arzikin ma an kasa samar da walwalar da mai karamin karfi zai iya samun natija, domin yau idan kana karban albashi naira dubu ashirin, za ka sai shinkafa buhu a naira dubu goma sha takwas ne, idan kuwa haka ne wace hanya za ka bi wajen rike iyalinka, akwai tsadar rayuwa kuma an kasa samo bakin zaren balle a walwale shi, tun bayan kammala zaben 2015 tattalin arzikin kasar ke kara tabarbarewa.

Ya kamata ‘yan Nijeriya su zauna su dubi wannan tsarin na tattalin arziki da ake tafiya akan shi, domin kasashen da suka cigaba ba sa makauniyar siyasa, duk wanda zai tsaya takara sai yazo ya baje kudurorinsa da muradunsa a faifai jama’a sun tantance ta hanyar dora su akan sikeli ayi masu tambayoyi kafin amincewa da su, idan mun dauki irin wannan salon ina da tabbaci a 2019 ba zamu sake irin wannan makahon zaben ba.

Ya kamata matasa mu zauna mu yi tunanin ta natsu kada idanun mu ya rufe, kar mu yarda mu sake ‘yan gidan jiya domin irin mutanen da muka zaba suke wakiltarmu a majalisar tarayya da na jahohi, da yau wadanda ke rike da kananan hukumomi idan ka duba mutane ne da ba su da kwarewa kuma ba su da ajanda koda suka zo kan kujerar wakilci, wani ma a tasha yake yana harkokinsa da guguwar Buhari tazo idanun mutane ya rufe suka samu wannan damar, shi yasa ba wani abun azo a gani a yankunan kananan hukumominsu.

Ya kamata mu sani cewar karamar hukuma itace tushen raya tattalin arzikin kasa idan aka samu matsala a karamar hukuma an samu matsala babba, ina baiwa matasa ‘yan uwana shawara a 2019 mu zabi mutanen da zasu iya tashi su fadawa gwamna gaskiya idan yayi ba daidai ba koda a wajen mitin ne, hakan ne kawai zai ceto dimukuradiyyarmu da kasar daga halin da ta samu kanta.

Exit mobile version