Abba Ibrahim Wada" />

Guinea Ta Cire Sunan Keita Cikin ‘Yan Wasan Da Ta Gayyata

Guinea Ta Cire Sunan Keita Cikin ‘Yan Wasan Da Ta Gayyata

Kociyan tawagar kwallon kafar Guinea, Didier Sid, ya cire sunan Naby Keita daga jerin ‘yan wasan da za su buga ma sa karawar sada zumunta a makon gobe a wasannin da tawagar za ta fafata.
Tun farko an saka sunan dan wasan mai shekara 24 cikin ‘yan kwallo 23 da za su buga wa Guinea fafatawar sada zumunta da kasar Comoros ranar 12 ga watan Oktoba da kuma kasar Chile kwana uku tsakani.
Kocin ya maye gurbin Keita, wanda ya ke jinyar mako shida, da Kamso Mara mai buga gasar kasar Jamhuriyar Czech haka kuma an bai wa Aguibou Camara goron gayyata a karon farko, domin maye gurbin Mohamed Mady Camara wanda ya yi rauni.
Sid wanda aka bai wa aikin horas da Guinea a watan Satumba, an dora masa alhakin kai kasar gasar cin kofin nahiyar Afirka da za a yi a shekara ta 2021 da na kofin duniya a shekarar 2022 wanda kasar katar zata katbi bakunci.
Guinea tana rukunin farko a wasannin neman shiga gasar kofin nahiyar Afirka da ya hada da kasar Mali da Namibia da Liberia ko kuma Chad haka kuma za ta fara karbar bakuncin wasan farko da za ta fafata da Mali ranar 11 ga watan Satumba, kuma karawar ta hamayya ce.

Exit mobile version