CRI Hausa" />

Gundumar Zheng’an Ta Sayar Da Kayan Kida Na Guitar Zuwa Sassan Duniya

Zheng Ming mai shekaru 42 da haihuwa bai taba tunanin samun odar sayar da guitar ba sai a sakamakon fuskantar cutar COVID-19 a gundumarsa dake yammacin kasar Sin. A yanzu haka, an kara sayar da kayan kida na guitar zuwa sassan duniya domin nishadantar da mutane da dama da suke zaman gida sakamakon cutar.

Kamfanin Zheng Ming yana cikin yankin masana’antar samar da guitar na kasa da kasa dake lardin Guizhou, inda kamar kowane kamfanin samar da guitar, yake kokarin samar da kayan da kasashen waje suke oda.
A shekarar 2013, gundumar Zheng’an da ta yi fama da talauci a baya, ta jawo jarin waje, kuma gwamnatin gundumar ta gabatar da manufofin goya masa baya, don haka ‘yan kasuwa na asalin gundumar, sun koma sun kafa kamfanonin samar da guitar. Ya zuwa yanzu, yawan kamfanonin samar da guitar ya kai 89, wadanda suke samar da guitar fiye da miliyan shida a kowace shekara, kamar rabin yawan guitar da ake samarwa sun fito ne daga wannan gunduma.
A halin yanzu, gundumar ta kawar da talauci ta hanyar cinikin guitar. Ban da wannan kuma, wasu kamfannonin samar da guitar suna kokarin canja tsarinsu, da kafa tambarin kamfani don kara samun ci gaba a wannan fanni. (Zainab)

Exit mobile version