Daga Rabiu Ali Indabawa
Mr. Di ya kuma ayyana cewa duk wani yinkuri na raba Taiwan da kasar Chana tabbas zai wargaje, duk da ‘yancin cin gashi kan da tsibirin ke da shi.
Shugaban kasar Chana Di Jinping ya yi amfani da kalaman kishin kasa masu karfi yau Talata a lokacin da yake jawabin rufe taron wakilan majalisar kasar.
Mr. Di ya fadawa wakilan jam’iyyar NPC kusan su 3,000 cewa Chana na kan hanyar cigaba.
Ya ce tarihi ya nuna, kuma zai cigaba da nuna cewa tsarin gurguzu ne kadai zai iya cetar kasar, kuma sai ta hanyar mutunta, da habbaka akidun gurguzu na ‘yan Chana ne kadai kasar za ta iya samun gagarumin sauyi.
Kafin a kammala taron, ‘yan majalisar dokokin kasar sun gabatar da kwaskwarima ga kundin tsarin mulkin kasar akan kawo karshen takaita wa’adin shugaban kasa da mataimakinsa, matakin da ya ba Di damar cigaba da mulki har illa masha Allah.