Daga Sagir Abubakar, Katsina
Sanata Abba Ali ne ya tabbatar da haka a wani shirin gidan rediyon Katsina a matsayin wani bangare na bikin cika Katsina shekara talatin kafuwa.
Sanata Abba Ali ya tunato cewa, gwagarmayar ta fito fili ne a lokacin da suka fito da tutoci da kwalaye dauke da sakonnin bukatar kirkiro Jihar Katsina a lokacin da tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo ke shugaban kasa a mulkin soja kuma ya ziyarci lardin Katsina.
Ya ce, a matsayinsa na shugaban kwamitin kirkiro jihohi da kananan hukumomi na Majalisar Dattawa, shi ne sanata na farko da ya mika bukatar kirkiro jihohi a kasar nan.
Ciki har da samuwar jami’o’i biyar, kamfanin mulmula karafa, gina hanyoyi da sauransu. Ya ce daga cikin matsalolin da ke addabar jihar nan sun hada da rashin samar da kudaden shiga ga gwamnati.