Gwagwarmayata Ta Zuwa Kasar Jamus Da Rayuwata A Kannywood – Haruna Cizo

Haruna Cizo

Wannan shafi ya zakulo muku fitaccen mawaki kuma shahararre wanda ya yi suhura a ‘kafar sada zumuntar zamani, wato Haruna Salisu, da aka fi sani da Cizo 1 Jamany (Haruna Cizo). Mawakin ya fayyace wa masu karatu irin gwagwarmayar da ya sha a yayin tafiyarsa kasar Jamus da sauran batutuwan da suka shafi rayuwarsa ta Kannywood. Ga dai yadda hirar ta kasance tare da Furodusa Yakubu Bala Gwammaja:

 

Masu karatu za su so sanin shin wai wanene Haruna Cizo?

Da farko dai sunana Haruna Cizo, sunan mahaifina Salisu, amma mutanen gari sun fi sanina da Cizo wan Jamani, kuma an haife ni a  Jihar Kaduna a Karamar Hukumar Zariya. Sannan kuma na fara karatun firamare a Zariya, daga baya kuma aka dauke ni aka mai da ni Kano wajen kanin babana, a can na yi karatuna  cikin Fagge, na yi karatun Alkur’ani mai girma. Bayan na yi wasu shekaru a Kano na dawo Kaduna Zariya na ci gaba da karatun bokona kamar yadda dama can na fara kuma na daina, to dai wannan shi ne a takaice.

Kuma a yanzu haka ba na Nijeriya ina nan kasar Jamus, domin na tafi na bar Nijeriya.

Abin da ya ja hankalina har na bar Nijeriya zuwa Kasar Jamus shi ne, da farko dai ni ban ma san kasar Jamus ba, kuma ban taba tunanin zan tafi kasar ba, na santa ne a 2014, a lokacin sun ci kwallon kafa, to a lokacin na san Jamus, domin ina da gidan kallon kwallo, kuma a wannan lokacin a ‘yan wannan shekarun a Nijeriya Boko Haram sun takura wa mutane suna kashe mutane haka kawai ba gaira ba dalili, a Masallatai da Coci, har barikin sojoji.

To a lokacin ni kuma gaskiya kawai sai na ga tun da muna harkar ‘Entertaiment’ ina da gidan kallon kwallo kuma ‘yan Boko Haram na kai hari, sai na ce to ni na gaji gara ma mutum ya bar Nijeriya ya ma huta da wannan kasar shikenan kawai na yanke shawara zan tafi Sudan.

Na hadu da wani abokina da muke buga kwallo tare da shi, sai ya ce za mu je wani Tim a Sudan. Dalilin wannan tafiyar to hanyar da ake bi a mota za mu je ba a jirgi ba, kuma ba mu samu biza ba an cinye mana fasfo dinmu da kudinmu da muka biya, sai muka ce to mu tafi a kasa ta mota, kuma hanyar da ake bi a maiduguri ce a yanke a tafi Sudan, ashe ‘yan Boko Haram an rufe hanya domin in sun kama mutane yankan rago suke musu, muka ce to yanzu ya za mu yi mun riga mun fito.

Sai abokina ya ce mu tafi Libiya, to ni a lokacin na san dai ina jin labarin Libiya, kuma na san ana fada a lokacin, sai abokina ya ce ba za mu je ba an kashe mutane, can ma fada ake yi a lokacin. Na ce ai Nijeriyar ma fada ake yi, kawai mu tafi Ale Galib ya kira wani abokinsa dan kamasho a Agadas Allah ya taimaki mutanen Agadas, muka je Agadas daga nan aka hada mu da wanda zai kai mu aka dauke mu muka shiga Sahara kwananmu bakwai a Agadas tukunna muka tuka mota Hilos a cikin Sahara, a Hilos ake tafiya, to kuma hanyar, hanya ce mai muguwar wahala ake bi cikin Sahara ruwa zai iya kare muku ko za ku iya hadari ko kuma Sahara ya taso da karfi ya ta rairaye ku gaba daya ku ga kun fada rami gaba daya ku mutu, ba abin da baya faruwa.

To haka dai muka bi hanyar satinmu guda ruwa ya kare mana, sai dai ka sha fitsarinka, abubuwa dai iri-iri ga yunwa, muka samu muka kai Libya da kyar, to bayan mun je Libya ma a can haka ma aka sayar da mu kamar yadda ake sayar da mutane, haka a Libya ake sayar da mutane za ka biya kudi mai mota ya dauke ka kuma ya je ya sayar da kai a je a yi ta dukanka a ce sai ka kawo kudi, kaga kamar garkuwa da mutane kenan, amma su a libya ana cewa ‘Gidan Bashi’.

Za a yi ta dukanka a ce sai ka kawo kudi, duk kwana kuma kudin na karuwa, to haka aka kai mu da kyar muka kwaci kanmu, muka biya kudi aka sake mu. Bayan na zauna a garin watana biyu na ji wahala, domin ni na ga larabawa a tunanina mutum idan ka tafi kasar larabawa za a tausaya maka irin za ka yi tunanin irin kasa ce ta Musulmi, to amman da na je naga su Larabawa ba sa son bakin mutum, a Masallaci ma balarabe ya taba dukana.

Tun a lokacin na fara kokwanto wai Addinin Musuluncin nan wai gaskiya ne ma dai ko kuwa dai?, ‘a yi hakuri da fadin haka’ Saboda na ga ni a lokacin ban waye ba sosai, ni a tunanina a lokacin muna ‘Africa’ in aka ce Balarabe in ka zagi Balarabe sai mu ce maka ka fita daga addinin Musulunci, sai da muka je muka ga ai abin nasu sai a hankali, to daga baya ne na kara wayewa na tuna ai da muna yara duk an koya mana Larabawan suna daya daga cikin wanda suka takurawa Manzon Allah (S.A.W), suka takura masa suka rika dukansa da jifansa da sauran abubuwa, muka ce to in ma sun yi mana ba matsala bace.

Daga baya da muka gaji muka ga abin na su ba wani kayan madallah na ji labarin ana tafiya daga ‘Libya’ zuwa ‘Italiya’ amma ta ruwa ta cikin teku kuma ana mutuwa, na ce ai mutuwa mutum ba zai guje mata ba, na je na yi ta aiki na tara kudade hannuna ya yi ta kanta ni ne aikin kwashe bola, ni ne aikin kwashe yashi, mu ne aikin zuwa gini, duk wani aiki da ka sani na wahala na ‘hadari’ shi na je na rika yi na tara kudina na biya kudin ‘Collection’ da ake biya wurin ruwa nan ma aka cinye min kudi na ci gaba da neman kudi na tara kudi.

Wallahi haka na zo na biya kudi, bayan na biya kudi na shiga muka shiga ‘Italiya.’ To Italiyan muna zuwa su ma na ga gaskiya abin na su ba wani kayan madallah na ga toh ai Italiyan ma sai a hankali, ban da lafiya ga shi bani da kudi gashi bani da magani, kawai wani ya ce ai ka tafi Jamus suna taimakawa mutane wani dan giniya ne, a wannan lokacin kawai sai na ce to, in dai haka ne ai kuwa sai na je Jamus din nan, haka na tafi ba ta kudi ba, aka nuna min tashar jirgin kasa, haka nake zuwa na je na zauna a cikin jirgin kasa tun daga Sisiriya har izuwa Jamus, sai da na yi sati biyu, kamar a ce ka tashi daga Lagos zuwa Kano ne kaga tafiyar kwana daya ne, amma sai da na yi kwana bakwai a hanya, saboda ba ni da kudi, ina zuwa na zauna a cikin jirgi idan kwanturo masu ‘tickiti’ sun zo “ina Tikitinka’ na ce ba ni da shi su ce na sauka, idan na sauka sai na jira awa biyu awa uku idan wani jirgin ya zo na kara hawa na Jamus, a haka a haka har fa na karaso na zo Jamani wallahi, na wuce Ostiriliya na zo Siwizalend daga nan na wuto.

Bayan na zo Jamus ban san kowa ba, sai na tafi gurin ‘yan sanda na ce musu ni bako ne daga afirika da dai sauransu, shi ne aka dauke ni aka taimaka aka kai ni ofishin hukumar shige da fice, daga nan da sauransu dai ka ji yadda aka yi na shigo Jamus.

 

Za mu ci gaba mako mai zuwa

 

Exit mobile version