Gwaman Bauchi Ya Karya Farashin Taki Zuwa ₦20,000
  • English
  • Business News
Wednesday, October 8, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Gwaman Bauchi Ya Karya Farashin Taki Zuwa ₦20,000

byAbubakar Sulaiman
1 year ago
Bauchi

Gwamnan jihar Bauchi, Bala Muhammad a ranar Asabar ya ƙaddamar da fara sayar da takin zamani na daminar bana kan farashi mai rahusa da nufin bunƙasa harƙoƙin noma a jihar. 

Da ya ke jawabi a wajen ƙaddamar da daminar bana da fara sayar da takin zamani a farashi mai rahusa da ya gudana a ƙaramar hukumar Dass, gwamna Bala ya ce, gwamnatin jihar ta sanar da Naira dubu ₦20,000 a matsayin kuɗin buhun takin zamani NPK guda.

Kazalika, gwamnan ya kuma ƙaddamar da sabbin Tiraktocin noma guda 60, sabbin Injunan noma domin ƙarfafa wa noman zamani, ƙari kan shirin tallafin kuɗi na dalar Amurka 25,000 ga zaɓaɓɓen ƙungiyoyin manoma a faɗin jihar.

  • An Ɗage Zaɓen Ƙananan Hukumomi A Bauchi
  • Kasar Sin Na Adawa Da Matakin Amurka Na Rattaba Hannu Kan Dokar Da Ta Shafi Yankin Xizang 

Muhammad ya ce a bisa ƙoƙarin da suke yi kan shirye-shiryen da suka shafi noma, gwamnatinsa ta shirya samar da wasu ƙarin kayayyakin noma da ɗaukan malaman gona domin inganta samun amfanin gona.

Gwamna Bala ya kuma nuna aniyarsa ta ilmantar da manoma da dabaru da hanyoyin amfani da sabbin na’urorin noma na zamani. Ya kuma ba da tabbacin cewa, za su yi duk mai yiyuwa wajen tabbatar da tsaro ga manoma domin ba su ƙwarin gwuiwar shiga gonaki domin noma ba tare da fargaba ko razani ba.

Ya nanata cewa gwamnatinsa ta ɗauki harƙar noma a matsayin abu mai muhimmanci lura da yadda yawancin ‘yan jihar suka kasance manoma.

Da ya ke jinjina wa gwamnatin tarayya da shirin inganta muhalli na bankin duniya wato ACReSAL da sauran abokan haɗaka, Gwamnan ya sha alwashin ci-gaba da shiga lunguna da saƙo domin nemo tallafi ga manoman da suke jiharsa.

Kan ɗumamar yanayi, gwamnan ya ce, za su shuka ire-iren shukoki daban-daban bisa shawarorin kwararru domin kyautata tattalin arziki.

Bauchi

Kan hakan, gwamnan ya yi gargaɗin cewa, duk wani mutum ko gungun mutane da aka samu da sayar da takin gwamnati kan farashi fiye da wanda ya sanar, to lallai mutum zai ɗanɗana kuɗarsa.

Tun da farko, Kwamishinan Ma’aikatar gona na jihar Bauchi, Farfesa Simom Madugu Yelams, ya ce, ma’aikatarsa ta ɗauki dabarbarun da suka dace wajen ganin noma da suke sassan jihar lungu da saƙo sun samu zarafin sayen takin ba tare da shan wahalhalun ba.

Shugaban riƙo na ƙaramar hukumar Dass, Muhammad Jibo, ya yaba wa gwamnan Bala Muhammad kan shirye-shiryensa na bunƙasa harkokin noma a faɗin jihar.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Kotu Ta Yi Watsi Da Ƙarar Da Aka Shigar Da Tinubu Kan Sanya Dokar Ta-Ɓaci A Ribas
Labarai

Kotu Ta Yi Watsi Da Ƙarar Da Aka Shigar Da Tinubu Kan Sanya Dokar Ta-Ɓaci A Ribas

October 2, 2025
Jam’iyyar PDP Ta Zaɓi Sabbin Shugabanni A Kwara
Siyasa

Jam’iyyar PDP Ta Zaɓi Sabbin Shugabanni A Kwara

September 28, 2025
Tinubu Zai Gana Da Manyan Ƴan Kasuwa, Zai Ƙaddamar Da Muhimman Aiyuka A Legas
Siyasa

Tinubu Zai Gana Da Manyan Ƴan Kasuwa, Zai Ƙaddamar Da Muhimman Aiyuka A Legas

September 27, 2025
Next Post
Wakilin Sin Ya Yi Kira Da A Tallafa Wa Kasashen Dake Yammacin Afirka Da Yankin Sahel Domin Lalubo Hanyoyin Samun Ci Gaba Da Suka Dace Da Yanayin Su

Wakilin Sin Ya Yi Kira Da A Tallafa Wa Kasashen Dake Yammacin Afirka Da Yankin Sahel Domin Lalubo Hanyoyin Samun Ci Gaba Da Suka Dace Da Yanayin Su

LABARAI MASU NASABA

Tinubu

Tinubu Na Son A Saka Hannun Jari Da Kuɗaɗen Fansho A Ɓangaren Mai Da Iskar Gas

October 8, 2025
Gwamnatin Nasarawa Za Ta Hukunta Duk Masu Amfani Da Sinadiran Kamun Kifi Acikin Ruwa

Gwamnatin Nasarawa Za Ta Hukunta Duk Masu Amfani Da Sinadiran Kamun Kifi Acikin Ruwa

October 8, 2025
Sin: Ana Sa Ran Jigilar Fasinjoji Fiye Da Miliyan 21 A Yau Ta Jiragen Kasa

Sin: Ana Sa Ran Jigilar Fasinjoji Fiye Da Miliyan 21 A Yau Ta Jiragen Kasa

October 8, 2025
Kwastam Ta Kama Lita 35,000 Na Man Fetur, Tabar Wiwi Da Sauran Kayayyaki A Kebbi

Kwastam Ta Kama Lita 35,000 Na Man Fetur, Tabar Wiwi Da Sauran Kayayyaki A Kebbi

October 8, 2025
Sin Ta Yi Kira Ga Mambobin WTO Da Su Tinkari Yanayin Tangal-Tangal Tare

Sin Ta Yi Kira Ga Mambobin WTO Da Su Tinkari Yanayin Tangal-Tangal Tare

October 8, 2025
ABU Na Kashe Sama Da Naira Biliyan 4 Duk Shekara A Wutar Lantarki

ABU Na Kashe Sama Da Naira Biliyan 4 Duk Shekara A Wutar Lantarki

October 8, 2025
Gwamnati Ta Roƙi ASUU Ta Soke Shiga Tsunduma Yajin Aiki, Ta Yi Alƙawarin Biyan Buƙatunsu

Gwamnati Ta Roƙi ASUU Ta Soke Shiga Tsunduma Yajin Aiki, Ta Yi Alƙawarin Biyan Buƙatunsu

October 8, 2025
Boko Haram Ta Taɓa Ayyana Buhari A Matsayin Wanda Zai Yi Mata Sulhu Da Gwamnati – Dalung

Boko Haram Ta Taɓa Ayyana Buhari A Matsayin Wanda Zai Yi Mata Sulhu Da Gwamnati – Dalung

October 8, 2025
A Kama Wani Likitan Bogi A Neja

‘Yansanda Sun Kama Masu Laifi 153, Sun Ƙwato Miyagun Ƙwayoyi A Jihar Jigawa

October 8, 2025
An Fara Biyan Ma’aikata Sabon Mafi Ƙarancin Albashin N70,000 A Borno

‘Yansanda Da Mutanen Gari Sun Daƙile Harin Boko Haram A Borno

October 8, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Exit mobile version