Daga Khalid I. Ibrahim, Bauchi
Gwamnan jihar Bauchi Muhammad Abdullahi Abubakar ya sallami Sakataren Gwamnatin Jihar Bauchi, Alhaji Bello Shehu Ilelah (mni) daga mukaminsa na SSG, hade da maye gurbinsa da Alhaji Muhammad Nadada Umar. Sanarwar dakatarwar gami da korar nasa ya fito ne daga gidan gwamnatin jihar Bauchi, wacce babban Sakatare kan aiyuka na musamman da harkokin siyasa, Sa’idu Abubakar Maikobi ya rattaba wa hannu kana aka raba wa manema labaru a ranar alhamis 20 ga July na shekara ta2017.
Wakazalika, Gwamnan Jihar ta Bauchi, ya kuma amince da dakatar da dukkanin kwamishinoninsa da kuma masu ba shi shawarori kan harkokin gudanar da mulki, illa mutum daya da gwamnan ya barsa a bisa kujeransa.
Sanarwar ta ce, Birgediya General Ladan B. Yusuf mai tallafa masa da kuma ba shi shawarori kan harkokin tsaro ne kawai wannan korar bata shafa ba, inda sanarwar ta ce shi na nan a matsayinsa na mai ba da shawara kan harkokin tsaro.
Shi dai sabon Sakataren Gwamnatin jihar Bauchi, Muhammadu Nadada Umar an haifesa ne a ranar 31 ga Disemba na alif 1954 a Dambam dake karamar hukumar Misau. Ya yi makarantar Firamarensa a garin Akuyam, sai ya je sakadarin gwamnati da ke Azare, kana ya je jami’ar Ahmadu Bello dake Zariya domin samun shaidar Digiri a fannin shari’a a shekara ta 1978. Ya yi aiki a ma’aikatu kamar su ma’aikatar shari’a daga 1978 zuwa 1980. Haka kuma yayi aiki a karkashin gwamnatin jihar Bauchi daga 1980 zuwa 1984, sai kuma ya yi aikin bankin New Africa Merchant. Ya taba rike mukamin sakataren gwamnatin jihar Bauchi a shekara ta 1999 zuwa 2006.
Sanarwar nan dai ta ce wannan kora da kuma canjin ya fara aiki ne nan take ba tare da bata wani lokaci ba. LEADERSHIP Hausa ta bayyana cewar sanarwar da aka raba wa manema labarum bai yi wani cikakken bayanin dalilin wannan kora da kuma dakatarwar ba.