Gwaman Bauchi Ya Yi Kira Da A Yi Rijistan Katin Zabe

Daga Khalid Idris Doya, Bauchi

Gwamnan jihar Bauchi Muhammad Abdullahi Abubakar ya kirayi al’umman jiharsa a cikin birni da karkara da cewar su hanzarta yin rijistan katin kada kuri’a na zabe, wanda ake ci gaba da yi a fadin kasar nan.

Gwamnan ya kuma ci gaba da yin kira ga al’umman jihar da suka rigaya suka yi rijistan katin da su hanzarta zuwa domin amsar shaidar da zai ba su damar zaben shuwagabannin da suke so a matakai daban-daban. Gwamnan jihar wanda ya bayyana hakan a sa’ilin da hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa reshen jihar Bauchi INEC suka kawo masa ziyara a karkashin shugaban hukumar a jihar Bauchi Alhaji Ibrahim Abdullahi a alhamis din da ta gabata.

Muhammad Abdullahi Abubakar ya sha alwashin cewar zai bada goyon baya wa kwamishinan hukumar zaben wajen gudanar da aikinsu ba tare da shiga musu cikin aikin nasu ba. Ya kuma bayyana cewar hukumar za ta yi aiki ne bisa tsarinta a jihar wajen gudanar da zabe ba tare da an yi mata katsalandan cikin sha’aninta na gudanar da zabe ba.

Gwamnan jihar, M.A Abubakar ya kuma baiwa hukumar ta INEC tabbacin samar musu da ingattaccyar tsaro a yayin da suke bakin aikinsu na tafiyar da harkokin zabe a jihar ta Bauchi. Ya kuma yi amfani da wannan damar wajen cewa akwai bukatar masu gudanar da zaben su yi la’akari da wadanda su ka dace wato masu shekarun da suka kai minzalin kada kuri’a.

Gwamnan ya kuma sha alwashin cewar gwamnatin jihar zata hada kai da INEC wajen fadakar da al’umma kan hidimar ta zaben da kuma yayada sanarwar yin rijistan ga jama’an jihar “Ina kira ga jama’a da su tabbatar sun karbi katinsu na zabe (PBCs) domin su samu zarafin kasancewa masu gudanar da zabe a yayin da ake zaben a kasar nan. Za mu taimaka wa INEC wajen yada sanarwar yin rijistan” a cewar Gwamnan.

A nasa jawabin, shugaban hukumar zabe mai zaman kanta a Jahar Bauchi, Alhaji Ibrahim Abdullahi, ya yaba wa gwamnan M.A Abubakar a bisa tabbar da samar da yanayin zaman lafiya mai kyau a jihar Bauchi a cewarsa hakan babbar abar nemace a ko’ina. Haka nan kuma ya bayyyana cewar hukumarsu za ta yi aiki da kwarewa wajen daidaita al’amura da kuma tafiyar da aikin nasu.

Shugaban na INEC ya ce sun kawo wa gwamnan ziyarar ce domin sanar da shi kan cewar sun fara aikin katin zabe a karo na biyu, inda ya ce suna bukatar gwamnatin jihar ta taya su sanar da jama’an jihar cewar ana aikin a karo na biyu.

Alhaji Abdullahi ya nuna bukatarsu ga kowani bangare na ‘yan siyasa da su tabbatar da fadakar da magoya bayansu muhimmancin yin katin zabe da mallakar katin zaben na dindindin a tsakaninsu. Ya bayyana cewar sama da mutunen jihar dubu sha biyar (15,000) ne ba su amshi katin zabensu ba a zagaye na farko da suka yi aiki, ya kuma koka da yawan adadin wanda suka fito a zangon aikin na farko, sai ya ce da bukatar gwamnatin jihar ta nusar da jama’a yin katin a akan lokaci kafin lokacin hakan ya kure . Ya kuma ce hukumarsu ta INEC tana shirye-shiryen fara gudanar da aikin rijistan a kananan hukumomin jihar guda 20. A bisa haka ya nuna bukatar ‘yan cikin garin dasu hanzarta yin rijista da kuma amsar katin nasu.

 

Exit mobile version