Idris Aliyu Daudawa" />

Gwaman Jihar Bauchi Bai Ji Dadin Yadda Fatara Ke Cigaba Ba A Jihar

Gwaman Jihar Bauchi

Gwamna jihar Bauchi Bala Mohammed a ranar Alhamis ce ya nuna damuwar sa kan yadda talauci yake kara addabar al’ummar jihar.

Mohammed wanda ya bayyana damuwar tasa ne a Bauchi a lokacin da yake rantsar da mutum takwas da aka nada kan mukamai daban-daban, ya ce ya kamata a yi abubuwa masu yawa ta hanyar shirye-shiryen rage talauci a jihar a shekarar 2021 don magance shi kalubalen da take fuskanta.

Gwamnan ya bayyana cewar yalu da akwai mazauna kauyuka da kuma birane da yawa wadanda suka nemi taimako daga gwamnati, kuma dole ne a taimaka masu da ‘sassauci’.

“Domin kawar da talauci wani abu ne wanda dole ne  ya yi yawa a shekara mai zuwa, saboda akwai mutane da yawa a cikin kauyuka, a cikin garuruwa, a cikin ma’aikatan jihar Bauchi wadanda ke bukatar wasu sassauci da kuma taimako daga gwamnati.

Ya cigaba da bayanin cewar “Mun fadawa mutanen mu na NIjeriya, musamman ma wadanda suka zabe mu a Bauchi cewar ba za mu gina hanyoyi kawai ba, har ma da gyara asibitoci, makarantu, da kuma aikin gona. Dole ne mu hada kai tare da sanin cewa talauci yana da yawa a jihar Bauchi.

“Dole ne mu yi hakan ta yadda zai a bada wani taimako da taimako ga mafi yawan mutanen da ke neman gwamnati ta taimaka masu”.

Gwamnan ya kuma ce da akwai bukatar ayi ma ita Hukumar da’ar Ma’aikata ta jiharayi mata gyaran fuska, ba kuam tare da wani bata lokaci bane sai ya bayyana nadin wasu kwararrun ma’aikata masu ritaya da za su taimaka wajen tsarkake ita hukumar kan rashin iya aiki, rashin gaskiya da kuma matsalar bata kamata ba.

 

“Muna bukatar yin abubuwa masu yawa don sake sanya jarinmu na dan Adam saboda akwai matsaloli da yawa a wannan yankin.

“Zan yi aiki tare da ku a 2021 don ganin yadda za mu magance  ita matsala ta rashin aiki, rashin tasiri da kuma rashin dacewa a tsarin, rashin gaskiya da dai sauran wasu abubuwa”.

Gwamnan ya yi alkawarin cewa kafin karshen gwamnatinsa, gwamnati za ta fitar ma’aikatan bogi wadandaake fitar da kudadeanan da basu kamata ba ta wata hanya. da sauran hanyoyin da suka dace don daukar mutane aiki a wasu ma’aikatun gwamnati.

Manema labarai sun bada rahpton cewar daga cikin wadanda gwamnan ya rantsar da akwai Danladi Danbaba a matsayin mashawarci na musamman kan rage talauci, Alhaji Yakub Barau a matsayin mashawarci na musamman kan raya Karkara, Nasiru Mohammed, mamba a Hukum daukar  da ma’aikata (CSC).

Sauran kuma sun hada da Yusuf Ibrahim, mamba CSC, Alh. Garba Babale, mamba, Kwamitin daukar ma’aikata na majalisa, CP Hamisu Makama (mai ritaya), mamba, Kwamitin bincike, Alhassan Musa, mamba, Kwamitin bincike, da kuma Alh. Abdullahi Maigari, mamba, Kwamitin bincike.

Da yake jawabi a madadin wadanda aka nada, Alhaji Danladi Danbaba, ya yaba wa gwamnan jihar kan yadda ya ba su amana sosai, yana mai kuma cewar za su yi iya kokarin su don taimaka wa gwamnatin jihar wajen sake dawo da jihar da kuma tabbatar da cewa ayyukan da gwamnatin yanzu ke yi an yi su ne kamar yadda ya kamata.

Exit mobile version