Daga Abubakar Abba
Kwamishinan Kudi na Jihar Akwa Ibom Nsikan Nkan ya yabawa Gwamnan Jihar Ibom Udom Emmanuel, saboda yin hadin gwiwa da Bankin Duniya don samar da ayyyukan da za su gina al’ummar jihar.
Nsikan ya yi yabon ne lokacin da wata tawaga daga Bankin na Duniya suka ziyarci jihar don duba wa da kaddamar da aikin Cibiyar kiwon lafiya da ke garin Ikot Akpa Edung, cikin karamar hukumar Ibesikpo Asutan.
Kwamishinan ya bayyana cewar, dakin shan maganin wanda shi ne na farko a yankin zai taimaka wajen rage kalubalen harkar lafiya da al’ummar yankin ke fuskanta.
Nsikan wanda shi ma dan asalin yankin ne, ya nuna jindadinsa a madadin al’ummar yankin a kan aikin na Bankin Duniya, inda ya yi nuni da cewa, fitowar da al’ummar yankin suka yi kwansu da kwarkawatarsu alamu ne na sun jidadi da aikin da aka kawo yankin.
Ya danganta kawo aikin da Bankin Duniya ya yi yankin a bisa ayyukan inganta taruyuwar al’umma da gwamnan ya kirkiro da su a jihar, inda kuma ya yi kira ga daukacin al’ummar jihar da kada su gajiya wajen bai wa gwamnatin jihar goyon bayan su har zuwa bayan da shekarar 2019.
Kwamishinan ya bayyana cewa, jihar cibiya ce ta zuba jari, inda ya roki tawagar ta Bankin Duniya da su yi amfani da damar wajen zuba jarinsu a jihar.
A nasa jawabin shugaban rikon kwarya na karamar hukumar, Barista Ukana Udofia ya gode wa Bankin na Duniya a bisa tagomashin da suka kawo yankin, inda ya tabbatar masu cewar za a yi amfani da dakin na shan magani kamar yadda ya dace.
Shi ma a nasa bayanin, shugaban kungiyar yankin, Dakta Sebastian Ibanga ya jinjina wa Bankin na Duniya aka ci gaban da suka kawo yankin, inda ya ce, dakin asibitin zai taimaka wa al’umar yanki matuka a kan harkar lafiyarsu.
Ya yi nuni da cewa, saboda rashin asibiti a yankin, yana haifar da rasa ran mata masu juna biyu a yankin, ya kuma yi roko ga tawagar na Bankin Duniya da kada su gajiya wajen kara samar da wasu asibitocin ga sauran kauyukan da ke jihar.