Bayanin hakan yana kunshe ne a cikin sanarwar da kakakin gwamnan jihar Mista Sola Fasure, ya fitar a garin Osogbo a ranar Lahadin data gabata, inda ya ce, Gwamnan jihar Rauf Aregbesola, ya sanar da cewar bashin za ‘a samo shine daga bankin manoma.
A cewar Aregbesola, manoman dake a kananan hukumomin Ola-Oluwa, Egbedore da Ejigbo, sune zasu amfana da bashin wanda kuma yake a karkashin shirin noma da ake kira (Anchor Borrowers) na babban bankin kasa CBN.
Gwamnan ya ci gaba da cewa, Majalisar Zartarwa ta jihar ta amince a karbo bashin kamar yadda ma’aikatar aikin noma da samar da abinci ta jihar ta bukata.
Gwamna Aregbesola a karshe ya ce, majalisar Zartarwar jihar ta kuma amince da naira biliyan biyu don sake sabuntawa da kuma gyara Kwalejojin fasaha na jihar guda tara, inda ya ce kwalejojin sune na garin Osogbo, Gbongan, Ijebu Jesa, Otan Ayegbaju, Osu, Iwo, Inisa, Ara da kuma na Ile-Ife, kuma kamfanin Skill G Nigeria Limited ne zai yi kwangilar aikin.