Gwamna Abdullah Sule Ya Ware Naira Miliyan10 Don Gyara Science School, Andaha

Membobin

Daga Zubairu M Lawal Lafia,

Gwamnan jihar Nasarawa Injiniya Abdullah Sule ya bayar da ummurnin gyaran Makarantar sakondire ta Kimiyya da Fasaha dake garin Andaha dake karamar hukuma Akwanga cikin jihar Nasarawa.

makaranta Science School ta garin Andaha tsohuwar makaranta ce mai tarihi, ita ce makarantar Kimiya da Fasaha kwara daya tak a karamar hukuma Akwanga.

Duk da tarihin da Makarantar take dashi tazama koma baya, sakamakon lalacewar da makarantar ta yi ta zamo kango babu mai gane cewa akwai ginin makaranta a wajen.

Malamai basu da Ofishin zama sai dai su zauna a karkashin Bishiya. Dakin kwanan Dalubai tankar shagon tara kayan tarkace.

Babu ruwan sha, babu makewayi, babu wutan lantarki, babu wadatattun dakunana karatu. Akwai Dalubai masu yawa a makaranta maza da mata, amma makarantar tana tattare da kalubale na barazanar rashin tsaro.

Babu kayana karatu amma manyan jihar sunyi halin ko ina kula rayuwar yara yana cike da bara zana. Duk da cewa makarantar kwanane amma babu katanga, kuma Dajine kowa na iya shiga ya wuce. Dalubai sai sunje kududufi mai nisan gaske a daji sannan su dibo ruwan sha.

Gwamnan ya kai ziyarar gani da ido inda kuma ya gana da masu ruwa da tsaki na yankin Akwanga.

Exit mobile version