Gwamna Al-Makura Ya Jinjina Wa Tsohon Sarkin Garaku

Daga Zubairu T.M.lawal lafia

Gwamnan Jihar Nasarawa Alhaji Umar Tanko Al-makura ya jinjina wa tsohon sarkin Garaku marigayi Mister Sylbster Ohoh Ayih wanda aka fi sani da suna Abaga Toni. Gwamnan ya yi jinjinar ne a wajen Taron jana’izar tsohon sarkin wanda ya gudona cikin makon nan a Garin Garaku da ke karamar hukumar Kokona ta Jihar Nasarawa.

Gwamna Al-makura ya bayyana Sarki Mister Sylbster Ohoh Ayih a matsayin gwarzon da ya kawo cigaba a masarautasa da ma yankin baki daya. Ya ce; “Mister Sylbster Ohoh Ayih abin tunawa ne a kowane lokaci kuma tarihi ba zai manta da shi ba a wannan jihar”.

Ya kara da cewa, wannan rashin ba al’ummar yankin Kokona kadai ya shafa ba ya shafi dukkanin al’ummar jihar da ma kasa baki daya musamman ma idon aka yi la’akari irin gwarzantakar marigayin a halin rayuwarsa.

Gwamna Umar Tanko Al-makura ya yi kira ga alummar garin Garaku da su yi koyi da dabi’un marigayin saboda kasancewarsa mutumin da ya tabbatar da zaman lafiya da hadin kan al’ummar garin.

Kazalika, ya ce sarkin ba shi da wani buri da ya wuce kullum ya ga al’umma suna zaman tare da samar da cigaba, sannan ya yi kira ga al’ummar masarautar da cewa idon sun tashi yin zaben sabon sarkin da zai gaji marigayi Mister Sylbster Ohoh Ayih su yi adalci su bai wa wanda ya cancanta kuma zabin al’umma.

Exit mobile version