Daga Zubairu T.M Lawal Lafia
A ranar Larabar da ta gabata ne Gwamnan Jihar Nasarawa Ahaji Umaru Tanko Al-makura ya ziyarci cibiyar koyar sana’a wadda uwargidon gwamnan Hajiya Salamatu Al-makura ke ginawa a kan titin Shandon da ke cikin garin Lafia.
Wannan cibiyar mai suna ‘Mac Cef’ , tana koyar da ‘ya’yan talakawa marasa galihu sana’o’in hannu kama daga saka zuwa gyaran gashi na mata da na maza da gyaran wayar hannu da walda da rini da dinki da kuma ilimin sarrafa kwamfuta da dai sauransu.
Ita idai wannan cibiyar kimanin shekaru shida kenan da samuwarta, kuma ta ya yaye dalibai da dama, sannan a tsarin cibiyar duk wanda ya kammala karbar horo akan tallafa wa mutum da wasu ‘yan kayayyaki saboda ya je ya bude tasa sana’ar don iya dogaro da kai.