Munkaila Abdullahi" />

Gwamna Badaru Ya Sha Alwashin Gudanar Da Gwamnatin Hadaka

A Jiya ne gwamna Muhammad Abubakar Badaru ya saba laya a karo na biyu a matsayin zababben gwamnan jihar ta Jigawa.

Haka shima sabon mataimakin gwamnan jihar Alhaji Umar Namadi ya karbi rantsuwa a matsayin mataimakin gwamna na Jigawa.

Da ya ke gabatarda jawabinsa bayan rantsadda shi a matsayin gwamnan a karo na biyu Alhaji Muhammad Badaru yayi alkawarin gudanarda mulki tareda kowa da kowa.

Gwamnan wadda ya share tsawon sa’a guda yana jawabi, ya ce babu ko shakka duk da kasancewar lokacin da ya karbi karagar mulki a karo nafarko sun gaji matsaloli da dama daga tsohuwar gwamnati gamida matsalar tabarbarewar tattalin arziki, amma duk da haka sunyi nasarar ciyarda jihar gaba.

Haka kuma ya karada cewa,a wannan karon ma da yardar Allah da hadin kan al’ummar jihar za su yi iya bakin kokarinsa domin sauke nauyin da suka dora masa.

“Duk da kasancewar mun sami karin hidundumu sakamakon karin albashin ma’aikata, amma da hadin kanku zamu yi amfani da kwalkwaletarmu domin ciyar da wannan jiha gaba” in ji gwamnan.

Daga karshe ya yaba wa kwamishinoninsa da sauran masu taimakasa gamida al’ummar jihar baki daya da suka bisa nasarar da ya samu. Sannan gwamnan ya yi addu’a tare da tawassali da kyawawan ayyukanmu a wannan wata mai alfarma na ramadan bisa Allah ya albarci wannan zagaye na biyu na wannan gwamnti.

Exit mobile version