Gwamna Bagudu Da Minista Malami Sun Sabunta Rajistarsu Ta Jam’iyyar APC

Daga Umar Faruk Birnin-Kebbi

A yau ne Gwamnan Jihar Kebbi, Sanata Abubakar Atiku Bagudu da Ministan Shari’a, Abubakar Malami sun sabunta rajistarsu ta Jam’iyyar APC a runfunan mazabunsu na zabe da ke Birnin-Kebbi Jihar Kebbi.

Sabunta rajistar ta biyo bayan rusa duk shuwagabannin Jam’iyyar APC tun daga na kasa har zuwa jahohi, kananan hukumomi da kuma na mazabu a duk fadin Nijeriya.

Gwamnan jihar, ya sabunta rajistarsa a mazabar Nasarawa 2, a runfar mai-Alelu da ke a kan Titin Atiku Bagudu da ke cikin garin Birnin-Kebbi, wanda ya kasance shi ne na farko a rumfarsa da kuma jihar kebbi baki daya.

Haka shi ma Ministan Shari’a, Abubakar Malami ya sabunta rajistarsa a mazabar Nasarawa 1, a runfar filin Mariya a shiyar fada da ke cikin garin Birnin-Kebbi.

Gwamna da Ministan, sun yi kira ga al’ummar Jihar Kebbi da su fito domin sabunta rajistarsu ta zaman su yan Jam’iyyar APC a jihar ta kebbi. Haka kuma sun nuna gansuwar su ga irin tsarin da uwar Jam’iyyar APC ta yi don sabunta rajista a duk fadin Nijeriya.

 

Exit mobile version