Umar A Hunkuyi" />

Gwamna Bagudu Ya Bada Gudunmawar Naira Milyan 30 Don Gina Coci

Gwamnan Jihar Kebbi, Sanata Atiku Bagudu, ya bayar da gudunmawar Naira milyan 30 ga al’ummomin Kiristoci da ke Masarautar Zuru domin su gina Coci-coci.

Shugaban reshen kungiyar Kiristoci ta kasa (CAN), Rabaran James Manga, ne ya bayyana hakan a lokacin da ya ke amsa tambayoyi daga manema labarai.

Ya ce, gudunmawar an bayar da ita ne domin Kiristocin da ke Zuru, su samu damar gina Coci-Coci da kuma kammala wasu ayyuka da suka sanya a gaba.

Manga ya bayyana cewa, wannan shi ne karo na farko da Kiristoci a Jihar su ka sami gudunmawar makudan kudi daga wani gwamna a tarihin Jihar.

A cewarsa: “An danka ma na kudin an kuma rarraba su a daidai gwargwadon bukatun cocina daban-daban.

Yawancin kudaden sun tafi ne a wajen aikin gina cocina a garin Zuru. Duk da gwamnatocin Jihar da suka gabata sun dan yi wani abu ga Cocina din, amma dai bai taba kai wa yawan hakan ba.

Ya ce baya ga wadannan milyan 30 din, Gwamna Bagudu da kansa ya kai ziyara ga cocina din a lokacin bikin Kirsimati da ya gabata domin taya Kiristoci din murna.

Audu ya ce, Gwamnan kuma ya bayar da gudummawar buhunan shinkafa, kayayyakin tufafi da sauran kayan abinci ga dukkanin Cocinan da ke cikin Jihar a lokacin Kirsimatin da ta gabata.

Ya yi kira ga gwamnan da ya tabbatar da ya saka Kiristoci din a cikin sabuwar gwamnatinsa, ya na mai bayanin cewa, “a shekaru hudun da su ka gabata ba a sami wakilicin Kiristoci ba a cikin gwamnatin. Wannan ya na daya daga cikin babban kalubalen Kiristoci a Jihar.

“Amma a wannan karon, muna roko ga gwamna Bagudu da ya sanya Kiristoc a cikin gwamnatin na shi. Muna yi masa addu’a. Coci ta aminta da gwamnatin na shi, za kuma mu ci gaba da yi masa addu’a domin samun nasarar gwamnatin na shi.

Exit mobile version