Gwamna Bagudu Ya Je Ta’aziyar ’Yan Nijar Da Ruwa Ya Cinye

Daga Umar Faruk, Birnin-kebbi

Gwamnan Jihar kebbi Sanata Abubakar Atiku Bagudu ya kai Gaisuwar Ta’aziya ga Shugaban kasar Nijar Muhammadu Yusuf amadadin Shugaban kasa Nijeriya Muhammad Buhari, a fadar Gwamnatin jamhuriyar Nijar da ke a Niyame a ranar Lahadi 17 ga watan Satumbar 2017.

Sanata Abubakar Bagudu ya samu tarba mai kyau daga takwaransa Gwamnan Jihar Dosso, Alhaji Musa Usman a garin na Dosso, bayan yada zango a garin na Dosso, Gwamna Musa Usman ya jagoranci tawagar Gwamnan na Jihar Kebbi zuwa fadar Shugaban kasar Nijar domin mika gaisuwar ta’aziya Ga Shugaban kasar Nijar Muhammad Yusuf amadadin Shugaban Muhammad Buhari kan bala’in hadarin jirgin ruwa da ya shafi ‘yan kasuwar, har  mutum 100 na garin Gaya a cikin yankin Dosso jamhuriyar Nijar a makon da ya gabata. Wadanda ke kan hanyarsu ta zuwa kasuwa a garin LOLO ta Jihar kebbi.

A jawabinsa na Ta’aziya Ga Shugaban kasar Nijar,  Gwamna Abubakar Atiku Bagudu ya ce ‘Mun zo ne wannan fadar Gwamnatin Nijar domin na wakilci Shugaban kasar Muhammad Buhari kamar yadda ya umurce ni da in zo domin mika ta’aziya ga gwamnatin Nijar, iyalan mamatan da kuma al’ummar kasar Nijar baki daya. Kan babban rashin da kuka yi na ‘yan uwanku, kuma ‘yan kasuwarku da suka samu hadarin Jirgin ruwa a kan hanyarsu ta zuwa kasuwar LOLO da ke cikin karamar hukumar mulki ta Bagudo a jihar kebbin Nijeriya.

Da yake  jawabinsa na godiya ga Gwamnatin Nijeriya da kuma  Gwamnatin jihar Kebbi, Shugaban kasar Nijar, Muhammadu Yusufu ya bayyana jin dadinsa kan irin halin kulawa  da soyaya da ke tsakanin kasashen biyu.

Ya ce: “Ko a lokacin da abin ya faru Shugaban Kasar Nijeriya, Muhammad Buhari ya kira ni a wayarsa ta hannu, ya yi min ta’aziyya. Kuma ya fada min cewa duk da haka zai turo da wakilansa zuwa Jamhuriyar Nijar, domin su yi mana gaisuwar ta’aziya.”

Exit mobile version