Gwaman jihar kebbi, Sanata Abubakar Atiku Bagudu ya yaba da yadda shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nada dan asalin jihar Kebbi, Alhaji Abubakar Sadik Yelwa a matsayin babban manajan darakta na hukumar bunkasa yankunan samar da wutar lantarki (HYPPADEC).
Sanata Abubakar Atiku Bagudu, Gwamnan Jihar Kebbi ne ya yi wannan yabo a yayin gudanar da bikin liyafar bankwana da aka shirya a jiya ga Sadik Yelwa a fadar Gwamnatin jihar ta Kebbi da ke Birnin Kebbi.
Bagudu ya ce” Shugaba Muhammadu Buhari nadin Sadik Yelwa wani namiji kokarin wurin zakulu Abubakar Sadik Yelwa don nadinsa sabon manajan darakta na sabuwar hukumar da aka kafa don bunkasa yankunan samar da wutar lantarki wato (HYPPADEC) na farko a hukumar, yana mai shawartar wanda aka nada ya tabbatar da ya yi aiki tukuru don sauke nauyin da aka dora masa na zama shugaban hukumar.
Gwamnan ya kuma nuna farin cikisa da yabawa ga Shugaba Muhammadu Buhari kan nada wasu ‘yan asalin jihar Kebbi da suka cancanta a cikin manyan mukamai a matakin Gwamnatin Tarayya.
Bagudu ya ci gaba da ambato wadanda shugaban kasa ya baiwa mukamai daga jihar ta kebbi, kamar Alhaji Atiku Bunu matsayina Kwamishinan a Hukumar tabbatar da bin tsarin daukar ayyukkan gwamnatin Tarayya wato (federal character commission), Alhaji Ahmad Sama, Kwamishinan a Hukumar Kula da Ma’aikata da tsarin gudanar da aikin gwamnatin Tarayya wato federal cibil serbice commission , Alhaji Hussaini Kangiwa a matsayin Shugaban Hukumar Kula da Nakasassu, Hassan Bello a matsayin shugaban hukumar kula da sufurin ta Jirgin Ruwa wato (Nijeriya shippers council), sai kuma Hassan Koko na Hukumar Tashar Jiragen Ruwa wato (Nijeriya Port Authority).
Sauran sun hada da Darakta janar a hukumar dauka da samar da ayyukkan yi ta kasa wato (National Directorate of Employment), Dakta Nasir Ladan Argungu yayin da yake fatan cewa majalisar dattijai za ta amince da nadin Farfesa Audu .A Zuru a matsayin kwamishina na Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta kasa (INEC) wanda zai wakiltar jahohin Arewa maso Yamman kasar nan.
Gwamnan dai ya bayyana kwamishinan filaye da gidaje Abubakar Sadik Yelwa irin ci gaban da ya samar a ma’aikar filaye da gidaje ta jihar Kebbi kafin barin gado, ya kara da cewa Alhaji Sadik Yelwa a mutum mai matukar girmamawa wanda ya ba da gudummawa ga ci gaban Jihar ta Kebbi a dukkan bangarori na aikin gwamnatin jihar bakidaya.
Bugu da kari ya ce Yelwa a lokacin mulkinsa a matsayin Kwamishinan filaye da gidaje ya bullo da ayyukan gine-gine da kuma tsarin rabon filaye ga al’ummar jihar guda dubu 22 wanda ya kamata a aiwatar tare da bullo da wani tsarin da ake Kira AGIS a Ma’aikatar filaye da gidaje yayin zaman shi Kwamishinan.
Da yake mayar da martani, sabon Manajan Daraktan na HYPPADEC, Alhaji Abubakar Sadik Yelwa ya gode wa gwamnan kan wannan dama da ya ba shi na yin aiki a cikin majalisar zartarwa ta jihar Kebbi, inda ya bayyana Gwamna Abubakar Atiku Bagudu a matsayin kwarzon jagoranci wanda ya baiwa Kwamishinan da sauran mukaraban sa damar gudanar da ayyukka a ma’aikatun su ba tare da wata matsala ba. Ya ci gaba da cewa gwamna Atiku Bagudu ya taimakawa rayuwarsa tun lokacin da yana karatu a jami’a har zuwa yau. Saboda haka ina godiya kwarai da gaske.
Daga karshe Sadik Yelwa ya kuma godewa gwamnan bisa ga irin goyon bayan da yake baiwa ma’aikatar filaye. Ya yi baiwa gwamnan tabbacin cewa Hukumar za tayi hada gwiwa da Gwamnatin Jihar Kebbi wajen aiwatar da shirye-shiryenta kan ayyukkan da zata gudanar.