Umar Faruk" />

Gwamna Bagudu Ya Rantsar Da Sabuwar Kwamishiniya A Kebbi

Gwamnatin jihar kebbi ta ratsar da sabuwar kwamishiniya a jihar a jiya a Birnin- kebbi.

Bukin ratsuwar an Gudunar da ita ne a cikin gidan gwamnatin jihar ta kebbi dake a Birnin Kebbi, Wanda babbar jojin jihar mai shari’a Elizabeth Asabe Karatu ta ratsar da ita sabuwar kwamishiniya Hajiya Ramatu Adamu Gulma, inda mai shari’a Abbas Ahmad yawa wakilta a wurin bukin rantsuwar a fadar gwamnatin jihar ta kebbi a jiya.

Sabuwar kwamishiniya Hajiya Ramatu Adamu Gulma tsohowar mai shari’a ce a kotun majastari da ke a birnin tarayya Abuja kana ta zama darakta a ma’aikatar shari’a dake Abuja kafin bata kwamishiniya a jihar kebbi.

Da yake jawabinsa bayan kammala bukin rantsuwar a fadar gwamnatin jihar, Gwamnan jihar Santana Abubakar Atiku Bagudu ya bayyana Jindadinsa ga sabuwar kwamishiniya Hajiya Ramatu Adamu Gulma kan irin gudunmuwar da ta bayar a gidan shari’a, inda yayi Kira ga kwamishiniyar cewa a jihar ta kebbi ana bukatar gudunmuwar ta a gwamnatin jihar kebbi a karkashin jagorancinsa.

Ya ci gaba da cewa gwamnatin jihar kebbi ta samu nasarori daban daban a cikin shekaru biyu zuwa na uku, inda ya cewa ko akwanan shugaban kasa Muhammad Buhari ya bayyana cewa jihar ta taimaka wurin ganin cewa an samar da abinci da kuma farfado wa da arzikin noma a kasar nan da kusan kashi tamanin.

Har ilayau ya godewa ‘yan majalisar zartawa da kuma na dokokin jihar kan irin gudunmuwar da suka bayar wurin ganin cewa an samar da ci gaba mai amfani a jihar ta kebbi da kuma kasa baki daya.

Daga karshe sanata Bagudau yayi kira ga shuwagabanin da masu ruwa da tsaki na cikin jihar da sumayar da hankalinsu ga ganin cewa masu saka hannun jari sun kara shigo wa cikin jihar domin kara samar da cigaban jihar kuma kasar Nijeriya bakin daya.

Exit mobile version