Connect with us

LABARAI

Gwamna Bagudu Ya Yaba Wa Mutanen Ganten Fadama Kan Kula Da Giwaye

Published

on

A jiya ne Gwamnan jihar Kebbi, Sanata Abubakar Atiku Bagudu ya yaba wa mutanen garin Ganten Fadama da ke a karamar hukumar mulki ta Bagudo da kuma zariyar kalakala itama a karamar hukumar KoKo-Besse dukkan su a cikin jihar ta Kebbi kan kokarin su na kare rayukkan wasu giwaye uku a dajin garin na Ganten Fadama da kuma na zariyar kalakala da aka fara ganin su. Inda suka shiga cikin jihar ta Kebbi daga janhuriyar Benin da ke da iyaka da jihar a yankin karamar hukumar Bagudo da kuma Dandi .
Gwamna Bagudu yayi wannan yabon ne yayin da yake gabatar da jawabin san a godiya ga jama’ar garin da kuma na zariyar kalakala da kuma dukkan sauran jama’ar da suka taimaka wurin ganin cewa an kare rayuwar giwayen guda uku da suka shigo cikin jihar , yayin da yakai zirayar gani da ido a garin na Ganten Fadama a jiya domin godewa jama’ar yankin da kuma yaba wa ga irin kokarin da suka yi kan kulawa da giwayen uku da suka shigo jihar ta Kebbi a cikin makon da ya gabata.
Haka kuma yace” makasudin ziyara ta shine in godewa mutanen Ganten Fadama da na zariyar kalakala ga irin kokarin ku na ganin cewa kun kare lafiya da kuma rayuwar giwayen da suka shigo jihar ta yankunan ku wadanda ake saran cewa sun zone daga janhuriyar Benin a cikin makon day a gabata, inda aka fara ganin su a garin zariyar kalakala da ke a karamar hukumar KoKo-Besse kafin kuma daga baya suka daga zuwa garin ku”. Kazalika yace “ ina son in yi amfani da wannan dama domin na isar da sakon shugaban kasa Muhammadu Buhari da kuma Mataimakin sa Yemi Osinbanjo kan gagarumin kokarin da kuka yi wurin ganin cewa kun kare rayuwar giwayen batare da an kashe su ba ko kuma yi musu wani rauni a jikin su”,inji shi.
Saboda haka shugaban kasa ke godiya da kuma jinjina ta musumman gare ku, haka kuma ina son inyi kira ga jama’ar yankin nan da a cigaba da kula wa da wadanda giwayen har sa koma kasar da suka fito lafiya batare da wata matsala ta same su ba. Har ilayau ya kara kira ga jama’ar da su taimaka ga bayar da bayanai kan giwayen ga shuwagabannin kananan hukumomin su da kuma sarakunan su domin gwamnatin jihar ta rika sanin yanayin da giwayen suke ciki har tsawon lokacin da suka koma kasar da suka fito.
Bugu da kari ya gargadi jama’ar yankin ta Bagudo game da kashen dabbobin daji musamman wadanan giwayen da suka shigo jihar nan ta Kebbi domin dabbobin daji ne dab a kasafai ake ganinsu ba kuma dabbobi ne da aka harantawa jama’a kasha su. Yace “ jama’a kada a kashe su ko a cutar da su domin duk wanda ya cutar da su zai fuskaci hukunci mai tsanani”,inji shi.
Shima wani shedun ganin da ido da LEADERSHIP A Yau ta zanta dashi mai suna Dantallo Gante yace” na ganan giwaye biyu suna kiwo a bakin gonar shinkafa mallakar kanfanin shinkafar Labana a tsallaken kogin ruwan Nija da ya gita a tsakani “, inji shi.
Har ilayau majiyar ta kara da cewa” damuwar mu bawai kiwon giwayen cikin gona ba , amma mutanen da ke shiga gonakin mu domin zuwa kallon giwayen sun taimaka wurin lalata amfanin gonar da muka noma musamman shinkafa da kuma gero a gonakin namu”,inji shi. Ya kuma ce “ muna saran cewa giwaye nan sun fito ne daga janhuriyar Benin “.
Shima sarkin Ganten Fadama wakilinmu ya samu zantawa dashi domin karin haske kan zuwa giwaye uku a garin na Ganten fadama , Alhaji Muhammadu Bello, ya bayyana cewa “ an fara ganin giwayen ne a garin zariyar kalakala da ke cikin karamar hukumar mulki ta KoKo-Besse kafin suka baro zuwa garin na wanda sun kwashe kimanin kwanaki uku ayu wanda kuma mutanen garin na na Ganten Fadama suyi iya kokarin su na ganin cewa sun kare rayuwar wadannan dabbobin daji batare da sun samu wata matsala ba”.
Daga nan ya ce “ bayan jama’ar garin sun gan giwayen a cikin gonakin su sai na dauki matakin sanar da shugaban karamar hukumar mu ta Bagudo Alhaji Muhammadu kaura Danhakimi Zagga domin sanar da gwamnatin jihar ta Kebbi domin daukar matakin da yadace.
Advertisement

labarai