Connect with us

LABARAI

Gwamna Bello Ya Bayyana Alhinin Rasuwar Dan Majalisar Dokokin Jihar Kogi

Published

on

A ranan larabar da ta gabata ne, Allah ya yi wa dan majalisa mai wakiltar mazabar Ibaji a majalisar dokokin jihar Kogi, Honarabul John Abah rasuwa, bayan ya yi fama da doguwar rashin lafiya.
Marigayin yana zangonsa na biyu ne a majalisar karskashin jam’iyyar APC bayan zango na farko a karkashin tutar jam’iyyarb PDP kafin ya sauya sheka.
A sakonsa na ta’aziyya, Gwamna Yahaya Bello ya bayyana alhini da kuma rashin jin dadinsa a bisa mutuwar marigayi John Abah.
A wata sanarwa da babban sakataren hulda da ‘yan jaridu na gwamnan, Malam Onogwu Muhammed ya sanya wa hannu a shekaranjiya laraba a birnin Lokoja, gwamna Bello ya bayyana marigayi Abah a matsayin jigo a jam’iyyar APC mai biyayya da kuma himma a jihar wanda gudunmawarsu wajen dorewa da ci gaban jam’iyyar ta APC bashi misaltuwa.
Ya ce marigayi Abah gogaggen dan majalisa ne wanda ya ba da gagarumar gudunmawarsa wajen ciyar da mazabarsa da kuma jihar Kogi baki daya gaba ta hanyar aiwatar gabatar da kudurori da dokoki dabam dabam da zasu inganta rayuwar al’umma.
Gwamna Bello har ila yau yace marigayi Abah ya taka muhimmiyar rawa wajen kyautata dangantaka tsakanin bangaren zartaswa da majalisar dokokin jihar.
Yace jihar za ta rasa dimbin basirarsa da hikimarsa da kuma gudunmawarsa a majalisa dokokin jihar.
Gwaman Bello daga ya jajantawa iyalan marigayin da shugaban majalisar dokokin jihar Kogi da sauran mambobin majalisar da kuma al’ummar mazabar  Ibaji a bisa rasuwar marigayi John Abah.
Gwamnan a karshe yayi addu’ar Allah ya jikan marigayin tare da baiwa iyalansa jimirin jure babban rashin da suka yi.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: