Gwamna Buni Ga ‘Yan Kasuwa: Ku Zuba Jari A Yobe

Yobe

Daga Khalid Idris Doya

Gwamnan Jihar Yobe kuma Shugaban riko na jam’iyyar APC, Hon. Mai Mala Buni, ya bukaci masu zuba hannun jari, daidaikun masu hannu da shuni da sauran ‘yan asalin jihar da suke zaune a kasashen waje da su zo jihar domin zuba hannun jari na tattalin arziki domin bunkasa jihar.

Buni wanda ke wannan bayanin a yayin da ke kaddamar da kantin saye da saidawa Shopping Mall wanda wani dan jihar Dakta Umar Majalam Ibrahim ya gina a Potiskum, shalkwatar karamar hukumar Potiskum.

Gwamnan ya bada tabbacin Gwamnatinsa na mara wa kungiyoyi da daidaikun mutane baya domin ganin sun dafa wa yunkurin Gwamnatin na bunkasa tattalin arzikin jihar.

“Cike nake da farin ciki na kaddamar da wannan ginin da aka gina da zimmar bunkasa tattalin arziki wannan yana nuni da cewa Dakta Umar Majalam Ibrahim (Zannah Dujuma of Tikau Emirate) ya yunkuro domin bada tasa gudunmawa wajen inganta tattalin arziki.

“Gwamnatin mu za ta cigaba da samar da yanayi mai inganci da zai karfafi masu zuba hannun jari da su zo domin zuba nasu hannun jarin tare da kyautata tattalin arziki da kara samar da hanyoyin shigan kudade.

“A bisa haka nake kara gayyatar masu hannun da shuni a ciki da kuma ‘yan jihar da suke zauke a kasashen waje da su fito su zo domin zuba hannun jari don kai Yobe zuwa mataki na gaba,” Buni ya kara.

Sannan kuma gwamnan ya nemi al’umman jihar da su kara himma da azama wajen yin addu’o’in da za su tabbatar da kyautata zaman lafiya da kwanciyar hankali domin kara samar da damarmakin da tattalin arziki zai habaku.

Mai mallakin sabon kantin saye da saidawa Shopping Mall, Umar Majalam Ibrahim, ya ce ya kai daukan matakin gina kanti mai shaguna 115 ne domin agaza wa kokarin Gwamnatin Jihar na kyautata harkokin kasuwanci a jihar.

Ya kuma Sha alwashin sake gina wasu hanyoyin da za a samar wa matasa ayyukan yi ta fuskokin daban daban.

 

 

Exit mobile version