Gwamna Buni Ya Bukaci Daukar Tsauraran Matakan Tsaro A Yobe

Daga Muhammad Maitela,

Gwamna Mai Mala Buni na jihar Yobe ya bukaci daukar sabbin tsauraran matakan tsaro a jihar.

Ya bayyana hakan a wani taro na musamman tare da masu ruwa da tsaki, a sabon kalubalen tsaro da jihar ke fuskanta, musamman a garin Gaidam da garuruwan da ke makobtaka da ita.

 

Da yake jawabi a taron, wanda ya gudana a babban dakin taro a gidan gwamnatin jihar da ke Damaturu, Gwamna Buni ya bayyana kaduwarsa dangane da harin da Boko Haram suka kai Geidam wanda ya ji sanadiyar rasa rayuka tare da tilasta wa al’ummar garin kauracewa gidajen su a cikin watan Ramadan.

 

“Har wala yau, kamar yadda kuka samu labari, na hadu da shugaban sojojin ma’aikatar tsaro ta Nijeriya, Janar Leo Iraboh da tattauna batun tsaro, matakan tsaro na musamman wajen tunkarar yaki da matsalar tsaro a Geidam, saboda yanayin wajen; wanda yankin yana kan zirin Tabkin Chadi kuma kan iyaka da jamhuriyar Nijar da Damasak ta jihar Borno, daya daga cikin yankunan da suka fi fuskantar barazanar Boko Haram.”

 

“Bisa ga hakan nake bai wa jihar mu hakuri, kasancewarta rashin gudanar da wannan taron da wuri, saboda taron da muka yi da shugaban ma’aikatan ma’aikatar tsaron Nijeriya, musamman kokarin kai daukin tsaro tare da tunkarar farmakin da Boko Haram suka kai a Gaidam.”

 

“Bugu da kari kuma, ina mai kara bayar da tabbacin daukar dukan matakin da ya dace wajen shawo kan wannan matsalar hare-haren da Boko Haram ke kai wa a garin Geidam, har wala yau da bunkasa aikin samar da tsaron baki dayan jihar Yobe. Sannan kuma muna da taro na musamman da shugabanin rundunonin sojojin Nijeriya yan kwanakin nan dangane da daukar sabbin matakan tsaro a Geidam da jihar Yobe baki daya.” In ji Gwamna Buni.

Exit mobile version