Gwamna Buni Ya Kaddamar Da Shago 6000 A Kasuwar Buni-Yadi

Gwamna Buni

Daga Muhammad Maitela Damaturu,

 

Gwamnan Jihar Yobe, Hon. Mai Mala Buni, ya kaddamar da sabbin shaguna 6000 wadanda gwamnatin jihar tare da hadin gwiwa da hukumar UNDP ta Majalisar Dinkin Duniya suka gina a kasuwar Buni-Yadi, a karamar hukumar Gujba da ke jihar.

 

Gwamna Buni shi ne ya bayyana hakan a jawabinsa ga dubban jama’ar da suka halarci bikin bude sabbin shagunan, ranar Litinin a Buni- Yadi.

 

Har ila yau, ya kara da cewa aikin gina kasuwar ya zo ne a karkashin ayyukan sake farfado da yankunan da matsalar tsaron Boko Haram ta shafa don sake inganta walwala da ci gaban jama’a bayan lafawar rikicin.

 

A hannu daya kuma, Gwamna Buni ya yi karin haske dangane da yadda aikin sake gina kasuwar zai farfado da harkokin kasuwancin da aka san garin da shi, wanda ya kasance hadakar ‘yan kasuwa daga jihohin Borno, Taraba, Adamawa da Kano.

 

“Wannan aikin zai farfado da ci gaban tattalin arziki a wannan yanki tare da bunkasa kudin shiga ga jama’a domin dawo da walwala, inganta yanayin rayuwa kamar yadda wannan gwamnatin ta kuduri aniya.” in ji shi.

 

Haka kuma Gwamna Buni ya umurci shugaban karamar hukumar ta dauki ingantattun matakai wajen ganin an bi hanyar da ta dace na raba shagunan ga wadanda suka cancanta.

 

Bugu da kari kuma, a Buni- Gari, Gwamna ya kaddamar da bude makarantar firamari (International Primary School) wadda kamfanin Shell Petroleum Debelopment Company (SPDC), hadi da gwamnatin jihar suka gina.

 

Yayin da ya bayyana cewa gwamnatinsa a shirye take wajen aiki kafada da kafada da sauran kungiyoyin tallafi don samun ci gaban jihar.

 

Sa’ilin da yake yaba wa hukumar SPDC dangane da wannan hubbasa, Gwamna Buni bukaci karamar hukumar ta samar da cikakken tsaro a makarantar.

 

Da yake tofa albarkacin bakinsa, Kwamishina Ma’aikatar Kula da Ayyukan Jinkai da Abubuwan da Suka Shafi Ibtila’i a jihar, Dakta Abubakar Iliya, ya ce makarantar ta kunshi rukunan ajujuwa (blocks) hudu da ajujuwa 16.

 

Ya kara da cewa baya ga wannan, akwai sashen gudanarwa, dakin gwaje-gwajen kimiyya, sashen fasahar sadarwa (ICT) tare da wutar lantarki mai amfani da hasken rana da rijiyar burtsatse da makamantan su.

Exit mobile version