Muhammad Maitela" />

Gwamna Buni Zai Bunkasa Makarantar Marayu A Yobe

Gwamnan jihar Yobe, Alhaji Mai Mala Buni ya yi alkawarin bunkasa makarantar yara marayu da suka rasa mahaifa, dalilin rikicin Boko Haram a jihar wajen gina dakunan kwana da ajujuwa. Ya ce zai kara kudaden gudanar da makarantar daga naira 500,000 zuwa naira miliyan daya (1,000,000).

Haka zalika kuma, ya yi kira ga masu sukuni a cikin al’umma- daidaiku da kungiyoyi wajen tallafa  wa marayu, musamman wadanda suka rasa mahaifan su ta dalilin rikicin Boko Haram, ya ce wannan shi zai rage radadin kaifin rashin mahaifa.

Gwamna Mai Mala ya bayyana hakan ne a lokacin da ya kai ziyara a cibiyar kula da marayu ta ‘Yetim Orphanage centre’ da ke Damaturu.

Har wala yau kuma, ya bayyana cewa daukar nauyin kula da marayu aiki ne da ya rataya ga kowa- saboda haka bai takaita ga wasu bgungun wasu mutane ba kadai.

“Marayu yayan mu ne, kuma dole mu nuna musu kauna tausayi ta hanyar kokarin biya musu bukatun su, kuma ba gwamnati ce kadai ya dace ta aiwatar da dashi ba, nauyi ne da ya hau wuyan kowa”. Inji shi.

Gwamnan ya yaba da wadanda suka yi tunanin kafa wannan cibiya ta kula da marayu, kana ya bukaci shugaban makarantar da ya tuntubi mukaddashin sakataren gwamnatin Yobe idan wata mukata ta taso wadda suke neman tallafi.

A nashi jawabin, ko’odinatan cibiyar kula da marayun, Malam Gambo Garba, ya yaba matuka dangane da kokarin gwamnatin jihar Yobe a  haujin.

A baya, gwamnatin jihar Yobe ta sake gyara cibiyar kula da marayun tare da basu kyautar mota kirar bas.

Exit mobile version