Gwamna Dankwambo Ya Hori Sarakunan Gargajiya Kan Zaman Lafiya

A bisa la’akari da mahimmancin Masarautun gargajiya wajen samar da zaman lafiya a tsakanin al’ummu, Gwamnan Jihar Gombe, Ibrahim Hassan Dankwambo, ya umurci Sarakunan gargajiya a Jihar Da su kasance masu sanya ido sosai wajen samar da zaman lafiya da kuma magance duk wani abin da zai iya haddasa rikici a cikin al’ummun na su.

A lokacin da yake karfafa Sarakunan a matsayin su na iyayen kasa, da su taimaka wajen zakulo duk wadanda ba su amince da halayen su ba a cikin al’ummun na su, Gwamnan ya kuma kiraye su da su mahimmantar da al’amurran da suka shafi jama’an su.

Dankwambo, ya yi wannan kiran ne a ranar Asabar wajen bikin nadin Sarkin Pindiga, Alhaji Mohammed Seyoji Ahmed, a garin na Pindiga, ya bukace su da su kasance masu sanya ido sosai a kan abin da ya shafi tsaro a Masarautun na su da ma Jihar baki-daya.

A cewar Gwamnan, yin wannan kiran ya zama tilas, musamman a bukatar da ake da ita na zaman lafiya a lokacin kamfen din ‘yan siyasa a wannan babban zaben na 2019.

Gwamnan ya kuma bayar da tabbacin gwamnati, na yin aikin da ya hau kanta na kare rayuka da dukiyoyin dukkanin al’ummun Jihar, ya kuma yi alkawarin fadada aikin samar da ruwa na Pindiga har zuwa wasu kauyakun da ke kusa da Masarautar.

Hakanan ya bayar da tabbacin kammala duk manyan ayyukan hanyan da ake yi a yankin nan ba da jimawa ba.

A jawabin sa jim kadan da karban Sandar Sarautan, Sarkin na Pindiga, Alhaji Mohammed Seyoji Ahmed, ya godewa gwamnan a kan damar da ya ba shi na sake yi wa mutanan sa aiki a matsayin Sarkin su, bayan da aka tube shi daga Sarautar shekaru 9 da suka shige, (2004 – 2013).

Ya kuma tabbatar wa da gwamnan goyon bayan sa ga gwamnatin Jihar, sannan ya yi kira ga dukkanin mutanan kirki na Masarautar da su hada hannu wajen tabbatar da zaman lafiya a Masarautar da kuma Jihar ma baki-daya.

Ya kuma yaba wa Gwamnan kan samar da hasken lantarki a garuruwa sama da 50 na Masarautar, wanda duk an kammala su tuni.

Alhaji Mohammed Seyoji Ahmed, yana daya daga cikin manyan Sarakunan Jihar ta Gombe masu daraja ta daya, ya yi shekaru biyar ne a kan karagar mulkin tun daga shekarar 2013. Ya gaji mahaifinsa a matsayin dagacin Pindiga a shekarar 1984, yana da shekaru 28 da haihuwa, a shekarar 2000 ne aka daukaka darajar Masarautar zuwa matsayin Sarki mai wukar yanka.

Sai dai, tsohon Gwamnan Jihar ta Gombe, Danjuma Goje, ya sauke Seyoji, daga Sarautar a shekarar 2004, ya kuma kore shi zuwa gudun hijira a garin Tula da kuma Gombe, babban birnin Jihar, tun daga wannan shekarar har zuwa shekarar 2013, a lokacin da Gwamna Dankwambo, ya sake dawowa da shi a kan karagar mulkin na shi.

Exit mobile version