Gwamna Dauda Lawal A Shekara 60: Inda Akwai Fata, Akwai Mafita
  • English
  • Business News
Wednesday, October 8, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Gwamna Dauda Lawal A Shekara 60: Inda Akwai Fata, Akwai Mafita

bySulaiman Bala Idris and Sulaiman
1 month ago
Dauda Lawal

Ba ni da kokwanto akan cewa, Dauda Lawal na ɗaya daga cikin gwamnonin da suka fi kowa kwarjini a Nijeriya. Amma abu ɗaya da nake yawan samun ƙalubalen bayyana wa mutane shi ne shekarun sa.

 

Mutane su kan yi ihun ‘kai!’ wasu kuma su kan kalli idona cikin wasa da dariya su ƙaryata ni. Duk saboda na bayar da sahihin bayanin da na tabbata ɗari bisa ɗari akan cewa Dauda Lawal zai cika 60 a ranar 2 ga Satumba, 2025 (wato yau).

 

Wani lokaci, na kan gaji da bayyani. Ko da a ƙarshe sun yarda da shekarun sa, wasu mutane suna cusa musu shakku daga baya. Wasu suna nuna cewa ya bayyana a matsayin matashi kuma yana gyara kan sa ne saboda yana da dukiya.

 

Kun tuna jita-jitar ake yaɗawa game wai arzikin sa ya kai Naira Tiriliyan 9? Kuma Mutane da yawa sun gaskata.

 

A matsayin sa na gwamnan jihar Zamfara, ina da abubuwa da yawa da zan iya cewa game da Dauda Lawal, musamman da yake ina cikin makusantan sa, mai yin aiki kafaɗa da kafaɗa da shi a matsayin kakakin sa sama da shekaru biyu.

 

A shekarun baya na yi rubuce-rubuce da dama a kan Dauda Lawal, ma’aikacin banki kuma mai taimakon al’umma.

 

Amma, yayin da ya cika shekara 60 a yau, zan so in fitar da wasu ’yan muhimman abubuwa da Dauda Lawal ya yi a matsayin gwamna, wanda ke mayar da Jihar Zamfara daga kufai da aka manta da ita zuwa babban birnin.

 

Dukkan abubuwan da mutane ke faɗi game da shi natsuwa, kamun kia, da tsabta daidai ne. Ya canja ɗabi’ar ma’aikata, musamman waɗanda ke gidan gwamnatin Zamfara, waɗanda ke aiki a kan kujerar mulki. Salon rayuwarsu ta canja, ba kamar da ba.

 

Gusau, babban birnin jihar, an gyara ta a matsayin cibiyar birane, kamar yadda ya kamata. An shimfiɗa titi tare da saka fitilu masu haske a ko’ina. Gusau, wacce ba ta da fitilun warware cunkoson ababen hawa a 2023 kafin zabe, yanzu haka tana da fitilun a duk faɗin birnin. Garin ya ƙawatu saboda a hankali ɗabi’un mutane yana canjawa.

 

A matsayina na mai fafutukar nuna ma’amala ta ƙwarai, ɗaya daga cikin manyan makarantun tunani na zamantakewar al’umma, na lura da yadda ƙa’idar ‘Kallo Ta Cikin Gilashi’ ta Charles Horton Cooley ke aiwatarwa a tafiyar Gwamna Dauda Lawal a Zamfara. Za ku iya cewa ta ya.

 

Kallo Ta Cikin Gilashi ra’ayi ne da ke bayyana yadda mutane ke yin tunanin kansu dangane da yadda suke tunanin wasu na fahimtar su. Ta hanyar hulɗar zamantakewa, mutane suna amfani da maganganun wasu a matsayin “madubi” don tantance ƙimarsu, ɗabi’a, da halayensu.

 

A da, abin da mutane ke gani game da Zamfara idan suka kalli madubi, shi ne halin da ake ciki na ƙaƙani-ka-yi, jihar da ’yan bindiga da talauci suka kusa kawar da ita. Ita ce ƙarshe baya da fannin ilimi da kiwon lafiya. Dauda Lawal, masanin kimiyyar siyasa, ya canja wannan labari ta hanyar haɗa ƙa’idojin zamantakewa na aiki da ma’amala mai kyau.

 

Jihar Zamfara da mutane ke gani a madubi a yanzu, jiha ce da ke takara a matsayin jiha mafi inganci a fannin tattalin arzikin cikin gida, ilimi, cibiyoyi masu tasowa, kiwon lafiya, da sauransu.

 

Aikin ceto na Gwamna Dauda Lawal ya bayyana a dukkan ƙananan hukumomi 14 na jihar Zamfara, ba wai a Gusau, babban birnin jihar kaɗai ba.

 

Waɗannan manyan ayyuka sun shafi sassa daban-daban, waɗanda suka haɗa da kiwon lafiya, ilimi, ababen more rayuwa, da sauran muhimman wurare masu.

 

Gwamna Lawal ya mayar da Babban Asibitin Anka zuwa wani katafaren asibiti na zamani mai ɗauke da na’urorin kiwon lafiya na zamani a ƙaramar hukumar Anka. An yi wa asibitin gyaran ciki da waje.

 

Gwamnatinsa ta kafa makarantar Tsangaya ta zamani a Ƙaramar Hukumar Gummi, makarantar da aka tsara don shigar da Almajirai cikin tsarin ilimi na zamani.

 

A ƙaramar hukumar Bakura, Gwamna Lawal ya gyara Kwalejin Kimiyyar Aikin Gona tare da samar mata da kayan aiki, inda ya samar da damarmaki ga matasa don bunƙasa sana’ar su ta noma — ƙashin bayan tattalin arzikin Zamfara.

 

A Ƙaramar Hukumar Bukkuyum, ya ɗaukaka darajar PHC Nasarawa Burkullu zuwa babban asibitin zamani da na’urori na zamani domin amfanin al’ummar yankin. Bugu da ƙari, ya bayar da kwangilar gina titunan garin domin haɗa dukkan garuruwan da ke cikin ƙaramar hukumar.

 

Gwamna Dauda Lawal ya gyara babban asibitin da ke Ƙaramar Hukumar Maru tare da cikakken kayan aiki. Asibitin, wanda a baya ya yi fata-fata, yanzu an gyara shi yadda ya kamata.

 

A Ƙaramar Hukumar Talatar Mafara, Gwamna Dauda Lawal ya ƙaddamar da aikin gina sabon babban asibiti, domin a halin yanzu asibitin ya lalace. Sauran ayyukan a Talata Mafara sun haɗa da gyare-gyare a Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta Jihar Zamfara.

 

A Ƙaramar Hukumar Maradun, Gwamna Lawal ya inganta tare da gyara babban asibitin Maradun, inda ya mayar da shi Cibiyar Kula da Lafiya ta Zamani mai ɗauke da duk wasu kayayyakin jinya na zamani. Ya kuma gyara babban asibitin Maru tare da samar da na’urori na zamani.

 

Hakazalika, a ƙaramar hukumar Kauran Namoda, Gwamna Lawal ya gyara babban asibitin Kaura Namoda tare da samar da kayan aiki, ya gina makarantar Tsangaya na zamani, ya kafa cibiyar koyar da sana’o’i da ta dace domin samar da ayyukan yi ga matasa, da kuma gina ƙarin gidajen kwana a Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta Kauran Namoda.

 

A Ƙaramar Hukumar Shinkafi, Gwamna Lawal ya amince da sake gina babban asibitin Shinkafi da kuma aikin sake gina makarantar Attahiru Bafarawa.

 

A Ƙaramar Hukumar Tsafe, Gwamna Dauda Lawal ya gyara babban asibitin Tsafe tare da samar da kayan aiki, ya kuma gudanar da gyaran gaba ɗaya na Makarantar Koyon Fasaha ta Tsafe, ya sake gina babbar tashar mota ta zamani ta Tsafe, da sake gina babbar kasuwa.

 

A Ƙaramar Hukumar Bungudu, Gwamna Lawal yana gina titin mahaɗa na Furfuri, titin Rawayya, aikin gyaran makarantar da aka amince da shi gaba ɗaya, da kuma aikin gyara da kayan aiki na makarantar sakandaren Ɗan Gwaggo.

 

Ina da abubuwa da yawa da zan faɗa, musamman game da dangantakar mutane da gwamna na. Na yi alƙawari zan yi shi a hankali, ba a lokaci guda ba. Yau rana ce da za a yi bikin mai nasara. Alhamdu lillah, barka da cika shekaru 60 ga mutum mai kyakkyawar zuciya.

 

Barka da Ranar Haihuwa, Oga!

 

Sulaiman shi ne kakakin gwamnan jihar Zamfara.

 

Fassarar MAHDI MUSA MUHAMMAD

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

GORON JUMA’A
Goron Juma'a

GORON JUMA’A

August 15, 2025
GORON JUMA’A 8-8-2025
Goron Juma'a

GORON JUMA’A 8-8-2025

August 8, 2025
2027: An Samu Ruɗani Kan Buƙatar Yi Wa ADA Rajista Don Ta Zama Jam’iyya
Goron Juma'a

2027: An Samu Ruɗani Kan Buƙatar Yi Wa ADA Rajista Don Ta Zama Jam’iyya

June 27, 2025
Next Post
Kyakkyawan Fata Kan Nasarar Yaki Da Akidar Mulkin Danniya A Duniya

Kyakkyawan Fata Kan Nasarar Yaki Da Akidar Mulkin Danniya A Duniya

LABARAI MASU NASABA

Kasar Sin Ta Yi Kira Ga Kasashen Duniya Su Hada Hannu Wajen Raya Harkokin Mata

Kasar Sin Ta Yi Kira Ga Kasashen Duniya Su Hada Hannu Wajen Raya Harkokin Mata

October 7, 2025
Wakilin Sin Ya Ba Da Shawarwari Uku Kan Yaki Da Ta’addanci

Wakilin Sin Ya Ba Da Shawarwari Uku Kan Yaki Da Ta’addanci

October 7, 2025
Cika Shekaru 25 Da Kafuwa: ACF Ta Jadadda Kudirinta Na Samun Hadin Kai Da Zaman Lafiya

Cika Shekaru 25 Da Kafuwa: ACF Ta Jadadda Kudirinta Na Samun Hadin Kai Da Zaman Lafiya

October 7, 2025
Sauyin Yanayi: “Damfara” Ko Gudun Sauke Nauyi?

Sauyin Yanayi: “Damfara” Ko Gudun Sauke Nauyi?

October 7, 2025
SSANU, NASU Za Su Gudanar Da Zanga-zanga A Faɗin Nijeriya A Ranar 9 Ga Oktoba

SSANU, NASU Za Su Gudanar Da Zanga-zanga A Faɗin Nijeriya A Ranar 9 Ga Oktoba

October 7, 2025
Daukacin Mambobin Majalisar Kare Hakkokin Dan Adam Ta MDD Sun Amince Da Kudurin Da Kasar Sin Ta Gabatar Kan Kare Hakkokin Tattalin Arziki Da Zamantakewa Da Al’adu

Daukacin Mambobin Majalisar Kare Hakkokin Dan Adam Ta MDD Sun Amince Da Kudurin Da Kasar Sin Ta Gabatar Kan Kare Hakkokin Tattalin Arziki Da Zamantakewa Da Al’adu

October 7, 2025
Ɓatan-dabon Naira Tiriliyan 210: Kamfanin NNPCL Ya Buƙaci A Ƙara Masa Lokaci

Ɓatan-dabon Naira Tiriliyan 210: Kamfanin NNPCL Ya Buƙaci A Ƙara Masa Lokaci

October 7, 2025
Tinubu

Tinubu Ya Nemi Amincewar Majalisa Kan Karɓo Bashin Dala Biliyan $2.347 Da $500m Na Sukuk 

October 7, 2025
Cikar Wa’adin AGOA Ta Nuna Ra’ayin Amurka Kan Afirka

Cikar Wa’adin AGOA Ta Nuna Ra’ayin Amurka Kan Afirka

October 7, 2025
Da Ɗumi-ɗumi: Yakubu Ya Miƙa Ragamar INEC Ga Agbamuche-Mbu A Matsayin Shugabar Riƙo

Da Ɗumi-ɗumi: Yakubu Ya Miƙa Ragamar INEC Ga Agbamuche-Mbu A Matsayin Shugabar Riƙo

October 7, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Exit mobile version