Daga Muh’d Shafi’u Saleh,
Gwamnan jihar Adamawa, Alhaji Ahmadu Umaru Fintiri, ya rattaba hannu kan kasafin kudin shekarar 2021, na sama da naira biliyan 140, jiya Asabar a gidin gwamnatin jihar.
Wannan ci gaban ya samu ne biyo bayan anincewar da majalisar dokokin jihar ta yi da kasafin ranar Alhamis.
Ya ce “ganin yawan matasa maza da mata yasa aka ware mu su sama da biliyan 16 a cikin kasafin kudin” inji Fintiri.
Gwamnan ya kuma godiwa mambobin majalisar dokokin jihar bisa muhimmin goyon bayan da su ka bashi, musamman nazarta da tabbatar da amincewa da kasafin akan lokaci.
Ya ce “mun morewa dama da goyon baya daga mambobin masalisar dokoki, wadanda su ka nuna bukatar jiha shi ne na farko kafin kowace bukata” ya jaddada.
Gwamnan ya ce kasafin da’aka yiwa take da ‘kasafin kaefafawa’ za’a tabbatar da ganin ya samu armashi ta fuskar ayyukan raya ci gaba ta bangarori da dama a jihar.
Ya kuma yi alkawarin dakushe matsalar tattalin da annobar korona ta haifar da nufin kyaktata rayuwar jama’ar jihar, ba tare da daukan mataki kan masu hannayen jari ba, ya ce manufar dimokradiyya tsayuwa kan bukatun jama’a.
Haka nan kuma gwamna Fintiri, yayi alkawarin samar da ci gaba a lungo da sakon jihar, domin tabbatar da ganin kowa ya amfana da mulkin dimokradiyya a jihar.