Gwamna Ganduje Ya Amince da Dokar Hukumar Asibitocin Kwararru Guda Biyu A Kano

Gwamnan Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje a rattabawa dokar inganta asibitocin Kwararru na Muhammadu Buhari da ke Gigingiyu da Kuma Asibitin kananan yara dake titin zuwa giodan adana namun daji (Zoo) hannu ta shekara ta 2018, an gudanar da wannan gagarumin aiki agaban Kwamitin shawara dake karkashin jagorancin Dakta Aminu Magashi. Alokacin bikin sa hannun Gwamna Ganduje ya tabbatarwa  da wadanda zasu jagorancin bayarda shawarwarin yadda za’a gudanar da a sibiotcinj biyu  cewa wadannan asibici za gadanar dasu ba kamar yadda ma’aikatan gwmanati ke gudanar da sauran asibiotici ba.

Gwamna Gandje yace wadannan asibitoci biyu maganar yajin aikin ma’aikata ba zai shafe suba domin an samar da kariyar doka a gare su, kamar yadda Gwamnati ta tsara a wadanan asibitoci batun yajin aiki  bashi da gurbi baki daya. Ya ce ya na daga cikin kokarin gwamnatin Ganduje na samar da ingantattun asibitoci domin samar da nagartattacciyar lafiya ga al’ummar Kano, domin rage fitar da jama’a ke yi zuwa kasashen wajen da sunan neman lafiya. Gwamnan Ganduje ya ce akwai wasu asibitocin da suke da aniyar shigowa Kano domin amfani da ingantattun kayan da aka samar a wadannan asibitoci. Haka zalika Gwamna Ganduje ya yabawa Majalisar dokokin Jihar Kano bisa samar da wannan doka da suka yi cikin kankanen lokaci,

Da ya ke gabatar da na sa Jawabin shugaban kwamitin bayar da shawarwari Dakta Aminu Magashi ya godewa Gwamna Ganduje da sauran ‘yan majalisar zartaswa na Jihar Kano, inda ya bayyanawa Gwamna cewa sun sadu da wasu likitoci a lokacin gudanar da wannan aiki da suke kasashen waje sama da shekara 20 zuwa 30, wadanda ganin wannan kokari na Gwamna yasa suka nuna sha’awarsu ta dawowa wadanan asibitoci biyu domin zuba jari.  Musamman yadda suka gamsu da tsare tsaren gudanarwa asibitocin kakashin Gwamna Ganduje. Ko shakka babu munyi farin cikin jin wannan ci gaba. Saboda haka sai Dakta Magashi ya kara yabawa kokarin Ganduje bisa kyakkyawan jagoranci musamman karasa ayyukan wadannan asibitocu biyu da akayi watsi dasu a baya.

Wannan doka da aka sawa hannu  ta bayyana yadda za’a samar da tsarin masu gudanar da harkokin asibitocin biyu, wanda suka suka hada da shugaban hukumar asibitocin da kuma sauran mambobin sa, dokar ta kuma fayyace mukamin shugabar Mata ta hukumar gudanarwa  tare da sauran mambobin da za’a zabo daga ma’aikatar Lafiya da Kudi, ya yin da sauran zasu kasance  daga hukumar nan mai lura da ka’idojin aiki, sai kuma ofishin sakataren gwamanti, Hukumar lura da ci gaban zuba hannun jari, kokiyoyin sa kai, bangarori masu zaman kansu, kungiyar akantoci, kungiyoyin Mata da sauransu.

Idan dai za iya tunawa ranar talata 27 ga watan Nuwamba shekara ta 2017 Gwamnan Ganduje ya kaddamar da Kwamitin da zai bada shawarwari karkashi Dakta Aminu Magashi wanda aka dorawa alhaki bayar da shawara kan yadda za’a samar da hukumar gudanarwa wadannan asibitoci biyu, daga cikin ayyukan kwamitin har da duba kasafin tsare tsaren gudanarwa hukumar, samar da tsarin duba yadda za’a gudanar da aikin, ginawa tare da samar da kayan aiki a asibitocin biyu, sai kuma samar da bayanan harkokin ci gaban lafiya da kuma gogaggun ma’aikata.

Tunda farko ana sa Jawabin Kwamishinan Lafiya na Jihar Kano Dakta Kabiru Ibrahim Getso ya tunawa Kanawa abubuwan da shugaban Kasa ya fada bisa Kokarin Gwamna Gnaduje na Kammala wadannan asibitoci biyu alokacin da ya ziyaci Kano domin bude asibitocin  ‘yan watannin da suka gabat. Ya ci gaba da cewa akwai jami’an lafiyar da suke da kwarewa matuka kan mashinan da aka samar a wadanna asibitoci, kamar MRI da Kuma 4D- Ultra Sound, ya yinda za’a horar da suaran ma’aikatan kamar yadda aka kawo kwararu daga waje domin horar dasu, Kamar yadda Babban Sakataren yada labaran Gwamna Abba Anwar ya shaidawa Jaridar Leadership A Yau.

Exit mobile version