Abdullahi Muhammad Sheka" />

Gwamna Ganduje Ya Bukaci A Hana Makiyaya Zirga-zirga Tsakanin Arewa Da Kudu

Ya Ce, Samar Da Matsuguni Zai Taimaka Wa Gwamnati Magance Laifuka

Kananan Hukumomin Jihar Kano

Gwamnan Jihar Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya bukaci a samar da wata doka da zata hana tafiyar Makiyaya daga Arewa zuwa wasu sassan kasarnan domin dakile matsalar fadace fadace tsakanin manoma da Makiyaya. Gwamnan ya bayyana Haka ne a garin Daura dake Jihar Katsina lokacin da yake zantawa da manema labarai.

Gwamnan ya ce, rikicin manoma da Makiyaya ba zai kare ba har sai an samar da dokar hana tafiye tafiyen dabbobi daga Arewa Zuwa Arewa ta tsakiya da kuma kudancin kasar nan.
Ya ce kiwo da Kuma dadaden rikici tsakanin manoma da Makiyaya zai zama tarihi idan aka samar da waccan doka kuma ta gara aiki.
Gwamna Ganduje yace Gwamnatin Jihar Kano tuni ta kama hanyar magance matsalolin da suke da alaka da wannan, sakamakon wannan Gwamnati ta ginawa Makiyayan matsuguni wanda ake Kira RUGA.
“Mun gina matsuguni Ruga domin tsugunar da Makiyaya a dajin dansoshiya wanda ke kan iyakarmu da Jihar Katsina wanda hakan ya bamu nasara dakile matsalar ta’addanci a wannan yanki.
“Saboda Haka, muka gina gidaje, sannan muna gina dam, muna kuma Gina wuraren Samar da ingantattun shanu, mun samar da asibitin dabbobi wanda tuni muka fara aikin gina gidajen Makiyaya.
“Abinda muke nema shi ne fakatar da tafiye tafiyen Makiyaya daga arewacin kasarnan Zuwa sauran sassan kasarnan.
“A Samar da Dokar da zata hana wannan, idan ba haka ba kuwa ba zamu iya magance matsalar rikicin manoma da Makiyaya ba sannan ba za’a iya hana sace sacen shanu ba wanda ke cutar damu,” inji shi.
Da yake tsokaci kan nadin sabbin shugabannin hukomin Tsaro cewa ya yi, muna fatan zasu ci gaba da aiki tare da Gwamnonin Jihohi wadanda suka san abinda jama’a ke bukata sannan suka dan duk wani wuri mai hadari dake yankunansu.

Exit mobile version