Abdullahi Muhammad Sheka" />

Gwamna Ganduje Ya Kaddamar Da Dakarun Yaki Da Korona 2,000 A Kano

Gwamnan Jihar Kano Dakta Abdullahi Umar Gamduje ya kaddamar da Dakarun lura da matakan kariya ga Annobar Korona 2000 a Kano. Hakan na cikin kokarin Gwamnatin Jihar Kano na dakile yaduwar annobar sakamakon karuwar yaduwar cutar zagaye na biyu a Jihar Kano.

Da yake kaddamar da Dakarun a fadar Gwamnatin Jihar Kano, Gwamna Ganduje yace, Gwamnatinsa ba zata zuba ido tana kallon mutane suna karya ka’idojin kariya ga yaduwar annobar ba, ya kara da cewa dakarun zasu yi aiki da Hukumomin Tsaro domin tabbatar da ganin ana biyayya ga matakan kariyar.
“Ayau muna kaddamar da Dakarun lura da kiyaye ka’idojin kariyar ga Annobar wadanda zasu taimaka mana wajen tabbatar da wayar da kai tare da fadakar da al’umma alokaci guda kuma su taimaka wajen hukunta wadanda suka gaza yin biyayya ga ka’idojin yakar annobar.
“Annobar Korona ta dawo a zagaye na biyu, don haka zamu sake dawo da dukkan matakan  da muka dauka da farko domin dakile yaduwar annobar.”
Mutane da yawa na mutuwa a wannan karo, don haka ba zamu jira muna kallon annobar na ci gaba da yaduwa a tsakanin al’umma ba.”
Ya ce, duk da cewa ba zata sake kaimu ga rufe gari ba, amma dai zamu kara kokari wajen bayar da dukkan goyon baya ga al’ummar da annobar ta illata tattalin arzikinsu, ya kara da cewa an shigar da dukkan masu ruwa  da tsaki domin  tabbatar da shawo Kan al’amarin.
A nasa bangaren shugaban Kwamitin karta kwana kan yaki da annobar Korona, Dr. Tijjani Ibrahim, ya ja hankalin jama’a su tabbatar da ganin suna kiyaye ka’idojin da aka gindaya, ya jadadda cewa annobar zagaye na biyu tafi ta farko hadari.
Ya ce, cikin Mutane 100 da ake gwadawa ana samun Mutane 13 suna dauke da cutar, Wanda hakan ke nuna karuwar adadin wadanda ke kamuwa da cutar.
“Kafin bayyanar zagaye na biyu na annobar Korona, sai da Jihar Kano ta kasance babu wanda ke dauke da cutar, amma yanzu gashi cikin mutane 100 da ake gwadawa ana samun mutun 13 wadanda ke dauke da cutar.
“Idan aka kwatanta da zagayen annobar na farko akwai ban tsoro kasancewar a wancan lokacin cikin mutane 100 da ake gwadawa Mutane 4 kadai ake samu dauke da cutar.”
Sarkin Kano, Alhaji Aminu Ado Bayero ya godewa Gwamnatin Jihar Kano bisa jajircewar ta wajen samar da ingantattun kayan kiwon lafiya ga al’umma, daga nan sai ya bukaci jama’a su tabbatar baiwa dakarun goyon baya wajen gudanar da ayyukansu.

Exit mobile version