Gwamnan Umar Abdullahi Ganduje na Jihar Kano, ya mika sakon ta’aziyyarsa ga Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso bisa rasuwar mahaifinsa, Alhaji Musa Sale Kwankwaso.
Mahaifin Sanata Kwankwaso, wanda shi ne dagacin Madobi, ya rasu ne a daren Alhamis, ya rasu yana da shekaru 93 a duniya.
A wata sanarwa da kwamishinan yada labaran jihar, Muhammad Garba ya fitar, ya ce Gwamna Ganduje ya jimamin samun sakon mutuwar, sannan ya kara da cewa za a dinga tuna marigayin da irin hikimarsa da dattako a matsayinsa na jagoran al’umma.
“A madadina da gwamnatin jihar Kano, ina yi wa Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso da Masarautar Ƙaraye ta’aziyyar wannan babban rashi.