Daga Abdullahi Muhammad Sheka, Kano
Duk da kalubalen da gwamnatin Dakta Abdullahi Umar Ganduje ke fuskanta, kama daga ‘yan adawar cikin gida da kuma matsalar tattalin arzikin kasa, ga kuma tulin basukan da aka gadarwa gwamnatin tasa, amma hakan bai sa shi yin kasa a gwiwa ba wajen kammala wasu manyan ayyuka da suka lakume biliyoyin Naira cikin shekara biyu da doriyar da ya yi a kan karagar mulkin jihar Kano ba. Babban darakatan Yada labaran gwamnan Malam Salihu Tanko Yakasai ya bayyana cewa, ko hasidin iza hasada ya san gwamna Ganduje ya zarta sa’a. Darkatan yada labaran na wannan tsokaci ne lokaci da gwamnan ke zagayen duba ayyukan da aka kammala a cikin shirye-shirye gwamnati na kaddamar da su. Ya ce yanzu haka al’umma sun ga irin kayan aikin da ake zuwa a asibitocin Giginyu da asibitin yara da ke kan titin gidan Zoo, wadannan asibitoci su ne irinsu na farko a tarihin Jihar Kano, wadanda aka zuba wa nagartattun kayan aikin da duniya ke yayi.
Yakasai ya ce Akwai mashin din da asibitin kwararru na Shika da ke Zariya kadai keda irinsa, amma gwamna Ganduje ya yi kokarin kawo shi don saukaka wa al’ummar Kano samun damar binciken cutuka masu hadarin gaske wadda a baya sai dai a fita da mara lafiya Turai. Asibitocin an fara aikinsu shekaru da dama da suka shude, amma wata gwamnatin ta yi watsi da aikinsu. Gwamna Ganduje wanda kullum abin da ke zuciyarsa shi ne kara tattalin dukiyar jama’ar Kano ya sa shi jibintar kammala aikin asibitocin biyu.
Baya ga harkar lafiya yanzu haka aikin katafariyar gadar kasar da gwamna Ganduje ya kirkira tuni ya kammala, tana nan a mahadar titin Panshekara da Madobi, idan ka jima rabon da ka shigo gari ta wannan bangaren, kuma aka yi dace cikin dare ka shigo to dole sai an yi maka jagora kafin fita daga wannan gadar, domin kaf kasar nan babu gada mai fuka-fukai irinta, gashi kuma an kawata ta da hasken wutar lantarki, inji Tanko Yaksai.
Wadannan ayyukan babu shakka jihar Kano ba ta taba samun wata gwamnati da ta kammala su a lokaci guda kuma ake shirin kaddamar da su ba, hakan ta sa inji kakakin fadar gwmanatin ta Kano, ake da kyakkywan zaton mai girma shugaban kasa Muhammadu Buhari ne zai bude wadannan ayyuka da ba a taba ganin irinsu a lokacin guda ba.