Gwamna Inuwa Ya Bai Wa Matan Gombe Damar Tsunduma Siyasa – Hauwa Sarki

HON. HAUWA ADAMU SARKI kansila ce mai wakiltar gundumar Dawaki a birnin Gombe a tattaunawa ta musamman da wakilinmu na jihar Yobe ya yi da ita, ta bayyana yadda Gwamna Muhammad Inuwa Yahaya ya bai wa matan jihar cikakkiyar damar shiga harkokin siyasa. Ga yadda tattaunawar ta gudana da Wakilin LEADERSHIP A YAU, MUHAMMAD MAITELA, kamar haka:

 

Da farko za mu so ki bayyana mana sunaki, matsayi da gari?

Assalamu alaikum, sunana Hon. Hauwa Adamu Saraki, kuma Alkyabbar Yariman Gombe, sannan kuma ni ce kansila Mai wakiltar gundumar Dawaki a karamar hukumar Gombe.

 

Ranki shi dade, kafin zama Kansila, ko akwai wasu ayyukan ci gaba kika taba yi wa al’ummar wannan gunduma taki?

Alhamdulillahi, akwai abubuwan da dama wadnda Ubangiji ya kaddareni da zamowa silarsu a cikin al’ummata, daga cikinsu akwai daukar nauyin marasa lafiya, musamman ta bamgaren haihuwa da kuma kanana yara, tare da kokari wajen taimaka wa yara mata zuwa makarantun boko da tallafa wa yan uwa mata wajen dogaro da kai ta hanyar sana’o’i.

 

Wasu za su yi mamakin yadda kike samu nasarar zama kansila a matsayinki na mace, me zaki ce kan hakan?

Wannan ba abun mamaki ba ne, ikon Allah ne, sannan kuma mutanen wannan gunduma; maza da mata ne suka yarda suka kawo mu, domin mu wakilce su. Kuma babu abinda zamuce sai dai mu roki Allah ya yi mana jagoranci.

 

A dan wannan kankanin lokaci, wadane kudurori kike dasu, a matsayinki ta kansila?

Alhamdulillahi, duk da cewa ba mu yi wani jimawa ba, wanda kwata-kwata watanmu daya ne da zabe. Amma duk da haka mun sami nasarori domin yanzu haka muna koyawa mata sana’o’i Kuma daga baya za a basu bashin kudin da za su inganta kasuwancinsu, sannan na samu nasarar daukar nauyin matasa 70 domin koya musu na’ura mai kwakwalwa wato ‘Computer’.

 

Wane kokari ki ke yi wajen ganin kin wayar da kan mata wajen shiga harkokin siyasa a jihar Gombe?

To, dama can fafitikar da muke yi kenan, kuma kullum idan mun sami wata dama, a mu’amalar yau da kullum tsakanin mu da yan uwan mu mata, ko a firarraki da muke yi a kafafen yada labarai da makarantu ko wurin aiki, na kan dauki damar wajen jawo hankalinsu tare da nuna musu faidar shigar mata fagen siyasa da sauran abubuwan ci gaba.

 

Ranki ya dade, ya za ki bayyana kokarin gwamnatin jihar Gombe, a fannin ci gaba?

Masha Allah, Alhamdulillahi, yanzu al’ummar jihar Gombe ta samu hazikin gwarzo Kuma jajirtaccen Gwamna, Alhaji Muhammadu Inuwa Yahaya, kuma ko shakka babu a wannan lokacin ne Gombawa mu ka shaida kan cewa ana mulkin dimukuradiyya, wanda ba mu taba samun dan kishin jihar Gombe da al’ummar ta ba kamar shi. Bugu da kari, duk mutumin da zai shigo jihar Gombe zai tabbatar cewa gwamnonin baya sun yi iya nasu kokari wajen shimfida ayyukan ci gaba, amma kuma ba su kai irin na Gwamna Muhammad Inuwa ba, saboda ayyuka ne wadanda su ka shafi ci gaban kowane bangare. Kuma dalilina shi ne, kowa ya san irin halin kunci da tattalin arzikin da duniya ya fada a ciki, wanda hatta manyan kasashen ma kuka sukeyi balle kuma kasar mu Nijeriya, wanda muka dogara kacokab kan man fetir da harajin cikin gida.  Wanda duk da wannan kalubalen, bai razana Maigirma Gwamna ba wajen gudanar da ayyukan ci gaban jihar Gombe ba, wanda gaskiyar magana wani zubin abun har zai baka mamaki, kowane lokaci sai shimfida tituna yake yi, gina asibitoci da gyaran wasu, makarantu, ruwan sha tare da tallafa wa mata da matasa, kyutata wa ma’aikata da walwalar jama’.

 

Ta wadane hanyoyi ne gwamnatin Inuwa Yahaya ta ke karfafa matan jihar?

Tabdijan, babbar magana, bari ka ji, Gwamna Inuwa “gwamnan mata kenan”, saboda gwamnatinsa ce kadai ta bai wa matan wannan jihar cikakkiyar damar a dama da su a harkokin mulkin jihar Gombe, wanda ko mace aka bai wa mulki iya gatan da za ta yi mana kenan. Saboda a cikin dukkanin nada mukaman da yake yi baya barin mata a Naya; mu na da kwamishinoni mata, shugabanin hukumomi mata, masu bashi shawara. Baya ga hakan, a lokacin wannan zaben kananan hukumomi ya yi tsayin daka wajen ganin an bai wa mata damar tsaya wa su fito takara. Kuma Allah ya ba mu nasara, wanda a halin yanzu muna da mace shugabar karamar hukumar Billiri, Magret Yusuf tare da kansiloli mata kusan a dukkanin kananan hukumomin Gombe.

 

Wacce rawa ce uwar gidan Gwamnan Gombe ke taka wa wajen ci gaban mata da matasa?

Ma sha Allah, ka tabo inda ke yi wa kowace mace a jihar Gombe kaikayi, saboda ko shakka babu wargida, Hajiya Asma’u Inuwa Yahaya ta cancanci yabo a wannan fanni kuma ta ciri tuta a tsakanain gwamnonin tarayyar Nijeriya. Matan jihar Gombe su na alfahari da kyawawan manufofinta tare da ingantattun shirye-shiryen ci gaban mata, musamman matan a yankunan karkara, mabukata da masu karamin karfi, ta fito da shirye-shiryen koya musu sanao’i’n da zasu dogara da kansu, kula da ilmin yara mata da sauransu. Bugu da kari kuma, yanzu haka akwai shirye-shirye na musamman da akeyi wanda za a horas da matasa fasahar zamani, kuma an tsara hakan ne domin ganin matasan wannan jihar sun samu hanyoyin dogara da kansu.

 

Wadanne kalubale Hon. Hauwa ke fuskanta?

To, kamar yadda kowa ya sani, ba a rabuwa da kalubale, sannan ba za a rasa ba, musamman irin yadda al’ummar yankin mu suka dauki siyasa a wajen ya-mace, saboda haka mun sha tsangwama da kyama. Amma Alhamdullahi, mu na ci gaba da kokari tare da fadakar da jama’a.

 

Wane ne babban burinki a rayuwa?

Allah abin godiya, babban burina a rayuwa shi ne ina son in zama wata abu a kasar nan; wato na shahara, kuma na kasance daga cikin shuwagabannin zartaswa, kudurin da nake dashi shi ne domin in jajirce wajen ganin an samarda dokokin da za su kyautata rayuwar matan Nijeriya baki daya. Ka na da tsayin daka wajen ganin an samar da ingantattun dokoki masu tsanani wajen hukunta masu aikata laifin fyade, sannan na bayar da gudumawa wajen inganta harkar ilmi, musamman na ’ya’ya mata. Har wala yau, ina da burin in ga na gina gidan marayu, saboda na lura cewa akwai karancin irin wadannan cibiyoyin kula da marayu a jihohinmu – wannan ya kara min karsashi.

 

Ko Hon. Hauwa tana da sako na musamman ga al’ummarta da jihar ta bakidaya?

Sakona ga al’ummar mu, musamman matasa shi ne lokaci ya yi wanda ya dace mu tashi tsaye don mu nemi sana’a, saboda yanzu lokaci ya wuce wanda kowa zai zuba ido sai gwamnati ta ba shi aiki saboda ya yi karatu da sauransu.

Exit mobile version