Daga Khalid Idris Doya, Gombe
Gwamnan Jihar Gombe Alhaji Muhammadu Inuwa Yahaya, ya gabatar wa shugaban kasa Muhammadu Buhari taswirar tsarin kafar cibiyar masana’antu da aka mata lakabi da ta ‘Muhammadu Buhari’ da gwamnatin jihar ta bada kwangilarsa.
Wannan matakin na zuwa ne a yayin wata ziyarar baya-bayan nan da gwamnan ya kai wa shugaba Buhari a fadarsa da ke Abuja, inda kuma suka tattauna kan muhimman batutuwa da suka shafi jihar da ma kasa baki daya.
A wata sanarwar da Ismaila Uba, kakakin gwamnan Gombe ya fitar, ya nakalto cewa, shugaban ya yi alkawarin bada goyon bayan gwamnatin tarayya ga kokarin gwamnan na tabbatar da tsaro da zaman lafiya dama bunkasa ci gaban tattalin arziki da zamantakewa.
Daga bisani gwamnan ya shaida wa manema labarai na fadar shugaban kasan cewa, idan aka kammala aikin cibiyar, ba kawai tattalin arzikin jihar za ta bunkasa ba har ma da samar da ayyukan yi ga dimbin matasa a ciki da wajen jihar.
Ya ce, “Mun tattauna kan batun cibiyar masana’antu wacce muka bada kwangilar gina ta da aka sanya sunan mai girmama shugaban kasa ‘Muhammadu Buhari’, na shaida masa haka kuma na nemi taimakonsa don ganin hakar mu ta cimma ruwa.”
“Mafiya yawan al’ummarmu kananan manoma da makiyaya ne, idan muka yi nasarar kafa wannar cibiya, zamu samar da manyan damammaki ga matasanmu a harkokin masana’antu da noma da sarrafa kayayyakin noman da kasuwancinsu dama rarraba su don su samu kyawawan hanyoyin dogaro da kai da habaka tattalin arziki.”
Gwamna Inuwa Yahaya ya ce, sun kuma tattauna kan matsalar tsaro, duba da cewa Jihar Gombe tana taka muhimmiyar rawa wajen karban bakuncin ‘yan gudun hijira daga jihohin Borno da Yobe da Adamawa wadanda rikicin Boko Haram ya shafa, lamarin da ke haifar da tsaiko ga ababen more rayuwa.