Gwamna Inuwa Ya Taya Kwamared Alhassan Murnar Zama Mataimakin Shugaban NUJ Na Kasa

Daga Khalid Idris Doya,

Gwamnan Jihar Gombe Muhammadu Inuwa Yahaya, ya cika da murna da farin ciki bisa samun labarin zaben Comrade Alhassan Yahaya Abdullahi a matsayin mataimakin shugaban Kungiyar ‘yan jaridu ta kasa NUJ.

 

Comrade Alhassan wadda kafin zaben sa a wannan matsayi shine mataimakin shugaban kungiyar (shiyyar E), an zabe shi ne tare da sauran shugabannin kungiyar na kasa da suka hada da shugaban kungiyar Mr. Christopher Isiguzo wadda aka sake zaba karo na biyu, yayin babban taron wakilai masu zaben shugabannin kungiyar na kasa da akan yi duk bayan shekaru 3, kuma ya gudana ne kwanakin baya a Jihar Abia.

 

A sakon sa na taya murna Dauke da Sanya hannun Malam Ismaila Uba Misilli Daraktan yada labarai Gwamnatin Gombe, Gwamna Inuwa Yahaya ya bayyana Comrade Alhassan Yahya a matsayin jakadan Jihar Gombe na kwarai kuma abun misali ga ‘yan jarida masu tasowa.

 

“Na cika da farin ciki matuka bisa wannan kyakkyawan labarin zaben dan uwan mu a matsayin mataimakin shugaban kungiyar ‘yan jarida ta kasa NUJ, babban matsayin da yake da tasiri matuka a aikin jarida.”

 

“Ina fatan zaka yi amfani da dimbin basirar da ka samu tsawon shekaru wajen samar da kyawawan manufofi da tsare-tsaren da za su kimtsa abokan aikin ka wajen dabbaka ka’idoji da dokokin aikin jarida musamman na tsage gaskiya, adalci, rikon amana da kishin kasa don gina al’umma ta gari”.

 

Da yake taya Kungiyar ta ‘yan jarida reshen Jihar Gombe murna na wannar daukaka da danta kuma tsohon shugaban ta ya samu, gwamnan ya jaddada himmatuwar gwamnatin sa na ci gaba da samar da kyakkyawan yanayin da ‘yan jarida zasu yi ta gudanar da ayyukan su yadda ya dace a jihar.

Exit mobile version