Gwamna Inuwa Yahaya Bai Ba Mu Kunya A Shekaru Biyun Mulkinsa Ba, Inji Nafada  

Gwamna Inuwa

KHALID NAFADA Wani fitaccen dan siyasa ne daga Jihar Gombe a hirarsa da LEADERSHIP A Yau, Lahadi ya bayyana cewar gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya ya fidda su kunya a idon Gwambawa cikin shekaru biyunsa a bisa karagar mulki, yana mai cewa gwamnan ya himmatu wajen sake fasalin Gombe domin gina rayuwar al’ummar jihar ta fuskacin shimfida kyawawan ayyukan raya birane da karkara. Ga hirar kamar yadda KHALID IDRIS DOYA wakilinmu a Gombe ya yi da shi:

 

 

Wani sako kake tafe da shi a yanzu?

 

Alhamdullah. Daga farko dai sunana Khalid Nafada daga jihar Gombe, kuma ni dan siyasa ne ina karkashin jam’iyyar APC wacce ke mulki a Jihar Gombe. Sakon da nake son fitarwa ga al’umma da ‘yan uwa da abokan arziki shine don mu tabbatar wa duniya cewa mai girma gwamnan Jihar Gombe, Alhaji Muhammadu Inuwa Yahaya a daidai lokacin da yake cika shekara 2 cif-cif a bisa karagar mulki kuma ya kawo abubuwan cigaba da yawan gaske wadanda ba za su kirgu ba kuma basu da adadi. A cikin shekaru biyun nan gwamnan ya samu nasarar gina manya da kananan tituna a cikin birane da karkara, ya samu nasarar bunkasa sashin ilimi, ya gina rayuwar matasa musamman ta fuskacin samar musu da ayyukan yi, bunkasa harkar noma da kiwo uwa-uba ga himmarsa wajen tabbatar da tsaro da kare rayukan jama’an Gwambawa, a takaice gwamna ya yi na mijin kokari sosai, kuma ya fitar da mu kunya.

 

A cikin nasarorin nan nasa meye ne za a iya cewa kai tsaye ya fi taba rayuwar al’umman Gombawa?

 

Eh to abubuwan da ya yi da suka taba rayuwar jama’a kai tsaye suna da yawa kamar yadda na fada maka tun da farko. Wadannan ayyukan raya al’umma da gwamnan ya yi ya riga ya shiga tarihi wanda ba za taba iya goguwa ba har-illa-Masha-Allah, gwamna ya yi kokari wajen kawo ci-gaba a fannin ilimi, ya kawo ciki gaba a fannin kiwon lafiya, sannan kuma ya kawo abubuwan bunkasa kasa irin su titina a birane, karkara, kauyuka da lunguna da sakunan jihar gaskiya kusan kowani fannin da dan adam ke da bukata gwamnan ya taba wajen yin ababen da suka dace domin ganin jihar ta kai zuwa mataki na gaba.

 

Akwai shirin gwamnatin Muhammad Inuwa na samar da hasken wutan kan layi mai amfani da hasken rana, wani alfanu kake hakan zai yi wajen bunkasa jihar?

 

Alfanun wannan shirin na da matukar yawan gaske saboda abun da ke faruwa duk abun da za a yi da zai ke kawo kudin shiga ko rage yawan kashe kudi kuma wanda zai kawo wa masana’antu saukin lamura wannan abun cigaba ne. idan ka duba wannan turakun wutar da ke amfani da hasken rana zai rage hayan kashe kudin gwamnati da kuma saukaka wajen sayen gas domin haska layukan kan hanya, akwai cigaba sosai ga samar da wannan shirin. Sannan wannan tsarin zai kara bunkasa jihar zai kyauta haskenta da kuma adonta, sannan kuma wasu kamfanoni a sakamakon wannan hasken wutar za su ji sha’awar zuwa domin zuba hannun jarinsu a jihar wanda zai baiwa matasanmu dama su samu ayyukan yi.

 

Kowace gwamnati na kokarin ganin ta samar wa matasanta ayyukan yi, akwai wasu shirye-shiryen da gwamna Inuwa ke yi don matasa kuwa?

 

Idan ka duba tun farkon zuwan gwamnatin Muhammadu Inuwa ta samar da tsare-tsare da shirye-shiryen da ta shirya domin matasa na tallafa musu wanda za a ke taimaka wa matasa da abubuwan yi, sannan akwai wasu shirye-shirye kuma da aka fito da su kamar rance wanda gwamnati ke dauke nauyin kaso kusan arba’in da dauri duk dai don a samar wa matasa abun yi da na tsayuwa da kafafu, a zahiri wannan gwamnatin tana maida hankali wajen kula da mata da matasa domin muhimmancinsu ga al’umma.

 

Wasu ‘yan adawa na korafin cewa gwamnatin nan ba ta tafiyar da mulki yadda ya dace me za ka ce a kai?

 

Wato abun da yake faruwa su dama ‘yan adawanmu na Gombe a kowani lokaci su adawarsu makauniya suke yi, su a kowani lokaci yadda za a yi su lalata gwamnati su batata shine a gabansu, muddin aka ce halastacciyar adawa kake yi dole za ka yaba wa gwamnati ta wani fuska, burinsu ina ne aka kasa su ce an gaza ba ina ne aka yi nasara su yaba ba. Mu kuma a kodayaushe muna yaba wa a wurin da aka yi da kyau, muna kuma nusar da gwamnati a inda muka hango kasawarta domin mu tayar da ita. Amma gaskiya mafi yawan ‘yan adawarmu na Gombe suna makauniyar adawa ce, duk wani abun alkairi da cigaba da mai girma gwamna ya yi su basu gani, burinsu su lalata da bata gwamnati kawai, domin neman su dawo mulki ta kowace fuska, su ba talaka ko jihar ne a gabansu ba, babban burinsu su dawo bisa kan mulki, kokarinsu kawai ya za su kawar da gwamnatin kirki shine a ransu, su samu dama su zo suna almubazarranci da dukiyarmu, suna sacewa da mana babakere. Mun ga irin rikon kwaryansu, sun zo sun mana abubuwa da yawa wadanda basu da wani amfani ga al’umman Gombe sun kashe kudinmu kawai ta hanyoyin da ba su kamata ba, sun dauki wasu ayyuka suka kashe maguden kudade amma ba kan ayyukan da talaka zai amfana ba.

 

Gwamnatin ‘yan adawa ta kasa bunkasa fannin kiwon lafiya da na ilimi, amma zuwan mai girma gwamna Inuwa Yahaya zuwa yanzu a dukkanin lunguna da sakona na kananan hukumomi babu inda bai gina karamar asibitin jinya ba; wanda su kuma a lokacinsu sun yi biris da wannan don ba kiwon lafiyan talakan bane a gabansu, sannan gwamna ya sanya dokar ta-baci a harkar ilimi dukka domin ganin an kyautata sashin ilimi da sauransu.

 

Akwai aikin tantance ma’aikatan bogi da a yanzu haka ake yi a jihar wanda ma har gwamnati ta bayyana wasu da take zargin ma’aikatan bogi ne tare da ciresu daga tsarin biyan albashi, ya kake kallon jihar Gombe bayan an kammala aikin tantance na bogin nan?

 

Kamar yadda na fada maka ne sakacin gwamnatin baya a kan harkar lafiya ya sanya har shigar da ma’aikatan bogi aka yi, ita gwamnatin da ta shude wasu daga cikin jami’anta azzalumai wadanda suke cin kudaden suka zo suka bada sunaye na karya da na bogi wanda daman zalumci shine a gabansu, daman su ba harkar lafiya da ilimi ne a gabansu ba, don haka basu damu ba in sun zuba ma’aikatan bogi a wadannan sashin. Don haka idan aka samu nasarar kammala bankado wadannan baragurbin, gwamnati za ta samu rara za ta samu damar daukan ma’aikatan da suka dace a sassa daban-daban domin rage yawan marasa aikin yi a cikin al’umma. A ma bisa kokarin gwamna ne har ka ga ana samun nasarar gudanar da ayyukan da suka dace, domin an bar mana basuka, an kuma shigar da ma’aikatan bogi, don haka rarar kudaden da aka samu sakamakon bankado wadannan ma’aikatan bogin ina tabbatar wa al’ummar Gombe cewa za a yi amfani da wannan damar wajen maye gurbin wannan ma’aikatan bogin da na zahiri wato wadanda suka dace.

 

A daidai lokacin da Gwamna Inuwa ya cika shekara biyu cif a bisa karagar mulki, wasu shawarori za ka ba shi a sauran shekarunsa biyu?

 

Gaskiya shawarar da nake baiwa mai girma gwamna, ya sani cewa akwai wata kalma da muke ta fada a duk inda muka je yakin neman zabe na ‘a gudu tare a tsira tare’, sannan kuma ya sani cewa mun yi amfani da wata kalma wanda za a yi walwala da yardar Allah, wancan gwamnatin da ta shude ba ta walwala sai dai wala-wala, wannan gwamnatin za a taimaka wa jama’a sosai kuma ‘yan siyasa za su ji dadinta, talakawa kuma za su gani a kasa kuma za su yaba. Mai girma gwamna ina son ka koma baya ka tuna da kalmar a gudu tare a tsira tare, mai girma gwamna ina son ka tuna wannan kalmar da kake cewa  ‘a hada tare a dauka a gina daki,’.

 

Zahirin gaskiya ta bangaren gina al’umma mai girma gwamna yana da dan nakasu, don haka nake bashi shawara da ya waiwayi baya ya duba ‘yan siyasan da suka masa wahala wadanda suke kaunarsa suke sonsa tsakani da Allah, wanda ya sani sun bashi gudunmawa bila-adadin da a yanzu suke zaune a gefe ba a waiwayarsu, don haka ina baiwa mai girma gwamna shawara da ya duba girman Allah ya duba a matsayinsa na shugaba, ya duba a matsayinsa na dattijo ya duba ya yi nazari a hadu a gina daki a daura gaba daya. Gwamna ina son ka tuna da kalamanka dai na baya. In ma ka son ka kyautata wa jama’a bayan shekara biyu ne to muna tuna maka a duba baya a duba wadanda suka bada gudunmawa, sannan a duba jama’an jihar, gwamna ka taimaka ka duba wahalar da wasu suka maka, batun kalmar walwala yana daga cikin abun da muka yaki gwamnatin baya da shi domin su ba a samu walwala a gwamnatinsu ba, don haka muna son a samu walwala da jin dadi a wannan gwamnatin, muna fatan mai girma gwamna zai kuma ji wannan bukatar ya yi abun da ya dace.

 

Daga karshe me za ka ce?

 

Muna kira ga al’umma da su kara sanya kasarmu a addu’a bisa irin wadannan fitintinu, masifu, rigingimu, da suke faruwa, duk da cewa mu babu irin wannan matsalar tsaron a wurinmu amma mu sani ‘yan uwanmu suna fama da matsalar mu cigaba da addu’a wa kasarmu, wuraren da suke fama da matsalar tsaro Allah ya yaye musu.

 

Mun gode!

 

Nima na gode.

Exit mobile version