Daga Lawal Umar Tilde,
Shugaban Gwamnonin Jihohin Arewa 19 kuma Gwamanan Jihar Filato Barista Simon Bako Lalong, ya bayyana kaduwarsa da samun labarin rasuwar dan majalisa mai wakiltar kana’nan Hukumomin Jos ta Arewa da Bassa, a majalisar wakilai ta tarayya a karkashin tutar jam’iyyar APC, Honarabul Haruna maitala.
dan majalisar dai Allah ya yi masa rasuwa da sanyin safiyar Asabar din da ta gabata a wani mummunar hadarin mota da ya yi a kauyen Gitata da ke kan hanyar Abuja zuwa Jos da yammancin Jumma’a.
Gwamna Simon Bako Lalong, a takardar da Darakta yada labarai na gidan gwamantin jihar Dakta Makut Mancham, ya rarraba wa kafofin yada labarai a Jos fadar gwamnatin jihar ranar Asabar, ya ce ya ji gwamnan yana cewa, “Mutuwar Haruna Maitala babban rashi ne ga iyalansa da mazabarsa da jihar da kuma kasa baki daya hakikan mun yi babban rashi.”
Gwana Lalong, ya kara da cewa wannan babban rashi ne ga majalisar dokoki na tarayya da gwamnatin tarayya, kasancewar ba a dade ba da rasa wadansu ‘yan majalisun tarayya bas ai ga rasuwar marigayi Haruna Maitala, wanda dan majalisa ne wanda ya nuna adalci a shugabancinsa kuma ya ba da ga garumar gudumuwa wajen ci gaban mazabarsa da jihar baki daya ya yi addu’ar Allah ya kyautata makomarsa ya bai wa iyalansa jumuriyar rashinsa.
Haka nan dan majalisa mai wakiltar Jihar Filato, ta Arewa Sanata Istifanus Gyang, ya nuna jimaminsa bisa samun labarin rasuwar. Honarabul Gyang, a cikin takardar ta’aziyya da babban jami’in Sakataren yada labaransa Mista Musa Ashom, ya rarraba wa ‘yan jarida a Jos a yammacin Asabar, ya yi Allah wadai da irin mummuna yanayin da hanyoyin mota na kasar nan su ka sinci kansu a ciki, musamman hanyar Abuja zuwa Jos, kuma ya bayyan marigayi Maitala, a masayin dattijo wanda ya yi tsayin daka wajen bauta wa al’ummarsa da kasa baki daya, ya yi fatan Allah ya yafe masa kaura- kuransa.
Wakilinmu da ke Jos ya ruwaito mana cewa dan majalisar ya rasu tare da dansa Jafaru Haruna Maital da direbansa da Odilinsa a cikin hadarin motar.