Gwamna Lawal Ya Rantsar Da Sabbin Shugabannin Kananan Hukumomi 14
  • English
  • Business News
Thursday, October 9, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Gwamna Lawal Ya Rantsar Da Sabbin Shugabannin Kananan Hukumomi 14

byLeadership Hausa and Sulaiman
11 months ago
Gwamna Lawal

Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal ya buƙaci sababbin zaɓaɓɓun shugabannin ƙananan hukumomin jihar da su bai wa al’ummarsu fifiko wajen tabbatar da adalci a gudanar da ayyukan raya jihar.

 

Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Jihar Zamfara (ZASIEC) ta bayyana ’yan takarar jam’iyyar PDP mai mulki a matsayin waɗanda suka lashe zaɓen dukkan kujerun shugabannin ƙananan hukumomi da na kansiloli da aka gudanar a faɗin jihar a ranar Asabar.

  • APEC: Nisan Wuri Ba Ya Hana Sada Zumunci Da Kulla Alheri Tsakanin Sin Da Kasashen Duniya
  • Kasashen Duniya Suna Sa Ran Jin Muryoyin Kasar Sin A Taron Kolin G20

A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sulaiman Bala Idris, ya fitar ta bayyana cewa an rantsar da zaɓaɓɓun shugabannin ne a yau Lahadi ta hannun Alƙalin Alƙalan Jihar Zamfara, Mai Shari’a Kulu Aliyu, a tsohon zauren majalisa da ke gidan gwamnati a Gusau.

 

Sanarwar ta ƙara da cewa, a yayin bikin rantsarwar, Gwamna Lawal ya yaba wa shugabannin Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Jihar Zamfara (ZASIEC) bisa shirya zabe na gaskiya da adalci.

 

Gwamnan ya jaddada cewa babban burin tsarin ƙananan hukumomi a Nijeriya shi ne kusantar da gwamnati ga jama’a tun daga tushe.

 

“Wannan yana da matuƙar muhimmanci a wannan lokaci, domin ƙananan hukumomi, a matsayinsu na mataki na uku na gwamnati, suna da matuƙar muhimmanci wajen ganin an samar da ingantattun ayyukan da gwamnati mai ci ke yi na ceto jihar daga matsalolin da suka shafi zamantakewa da tattalin arziki da kuma matsalolin tsaro da suka addabi sassan jihar.

 

“Saboda haka, akwai buƙatar haɗin kai tsakanin Majalisun Jihohi da Ƙananan Hukumomi don ƙara habaka cigaba a matakin farko, wanda hakan zai sanya jihar gaba ɗaya ta kasance kan turbar cigaba da wadata.

 

“Ina kira gare ku da ku kalli zabenku a matsayin kira na yi wa al’umma hidima ta hanyar ba da fifiko ga jin daɗin jama’arku da tabbatar da adalci wajen gudanar da ayyukan raya ƙasa. Kamata ya yi a cimma hakan ta hanyar amfani da shirye-shirye daban-daban na zuba jari da sauran tsare-tsare masu kyau da gwamnati mai ci ta bullo da su domin samar da ayyukan yi ga ɗimbin matasan mu, da samar da su da abubuwa masu amfani, da kuma daƙile aikata munanan laifuka da suka addabi jihar. Za a iya cimma hakan ne kawai idan kun rungumi gaskiya, riƙon amana, da taka-tsantsan wajen sarrafa dukiyar al’umma.

 

“Dole ne ku haɗa kai da Gwamnatin Jiha, musamman idan aka yi la’akari da tanade-tanaden Kundin Tsarin Mulkin 1999 (wanda aka yi wa kwaskwarima). Gwamnatin Jiha za ta ci gaba da haɗa kai da kansilolinku domin cimma burinmu tare da samar da haɗin kai don ci gaban jiharmu mai daraja”.

 

Gwamna Lawal ya kuma buƙaci zababbun shugabannin da su riƙa hulɗa da al’ummarsu yadda ya kamata.

 

“Ya kamata ku kafa hanyoyin sadarwa masu inganci, waɗanda ke da muhimmanci wajen fahimtar buƙatun mutanen da ku ke yi wa hidima.

Gwamna Lawal

“Ya kamata shugabancin ku ya ƙunshi tausayi da haɗa kai da jama’a ta hanyar tabbatar da cewa babu wani bangare na al’umma da aka bari a baya. Ya kamata a ba da kulawa ta musamman ga mutane mafi rauni – mata, yara, masu buƙatu na musamman, da kuma tsofaffi.

 

“Ina jaddada muku cewa bai kamata ku kebance ayyukanku daga Gwamnatin Jiha ba. Kun kasance wani muhimmin bangare ne na mulki. Don haka, ana sa ran za ku daidaita manufofinku da shirye-shiryenku daidai da abubuwa guda shida na wannan gwamnati: Tsaro, Ilimi, Noma da Tsaron Abinci, Ci gaban Tattalin Arziki, Bangaren Kiwon Lafiya, da Samar da Ababen More Rayuwa.

 

“A dangane da haka, ya zama wajibi ku ƙirƙiri ɗabi’a ta gaskiya da riƙon amana a dukkan harkokin ku. Ku tabbatar cewa kun adana bayanan kuɗinku da kyau kuma ana duba su lokaci-lokaci. Wannan zai ƙara sahihancin gwamnatocinku, ya kuma sa jama’a su aminta da shugabancinku.”

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Tinubu
Manyan Labarai

Tinubu Na Son A Saka Hannun Jari Da Kuɗaɗen Fansho A Ɓangaren Mai Da Iskar Gas

October 8, 2025
Kwastam Ta Kama Lita 35,000 Na Man Fetur, Tabar Wiwi Da Sauran Kayayyaki A Kebbi
Manyan Labarai

Kwastam Ta Kama Lita 35,000 Na Man Fetur, Tabar Wiwi Da Sauran Kayayyaki A Kebbi

October 8, 2025
Boko Haram Ta Taɓa Ayyana Buhari A Matsayin Wanda Zai Yi Mata Sulhu Da Gwamnati – Dalung
Manyan Labarai

Boko Haram Ta Taɓa Ayyana Buhari A Matsayin Wanda Zai Yi Mata Sulhu Da Gwamnati – Dalung

October 8, 2025
Next Post
Muhimman Abubuwa 7 Game Da Raya Huldar Sin Da Amurka

Muhimman Abubuwa 7 Game Da Raya Huldar Sin Da Amurka

LABARAI MASU NASABA

Tawagar Likitocin Sin Dake Saliyo Ta Gudanar Da Tiyatar Dashen Yatsa Irinta Ta Farko

Tawagar Likitocin Sin Dake Saliyo Ta Gudanar Da Tiyatar Dashen Yatsa Irinta Ta Farko

October 8, 2025
Babban Yankin Sin Ya Soki Lamirin Kalaman Aware Na Jagoran Yankin Taiwan

Babban Yankin Sin Ya Soki Lamirin Kalaman Aware Na Jagoran Yankin Taiwan

October 8, 2025
Yawan Zirga-Zirgar Jiragen Kasa Tsakanin Sin Da Turai Kan Layin Dogo Na Tsakiya Ya Zarce 3,000 A Bana

Yawan Zirga-Zirgar Jiragen Kasa Tsakanin Sin Da Turai Kan Layin Dogo Na Tsakiya Ya Zarce 3,000 A Bana

October 8, 2025
Majalisa Ta Nemi Jami’an Tsaro Su Ceto Daliban Jami’ar Gusau 30 Da Aka Sace

Kafa ‘Yansandan Jihohi Na Da Matuƙar Muhimmanci Wajen Magance Matsalar Rashin Tsaro

October 8, 2025
Adadin Kudaden Da Gidajen Sinima Na Sin Suka Tara Yayin Hutun Bikin Ranar Kasa Ya Haura Yuan Biliyan 1.7

Adadin Kudaden Da Gidajen Sinima Na Sin Suka Tara Yayin Hutun Bikin Ranar Kasa Ya Haura Yuan Biliyan 1.7

October 8, 2025
Tinubu

Tinubu Na Son A Saka Hannun Jari Da Kuɗaɗen Fansho A Ɓangaren Mai Da Iskar Gas

October 8, 2025
Gwamnatin Nasarawa Za Ta Hukunta Duk Masu Amfani Da Sinadiran Kamun Kifi Acikin Ruwa

Gwamnatin Nasarawa Za Ta Hukunta Duk Masu Amfani Da Sinadiran Kamun Kifi Acikin Ruwa

October 8, 2025
Sin: Ana Sa Ran Jigilar Fasinjoji Fiye Da Miliyan 21 A Yau Ta Jiragen Kasa

Sin: Ana Sa Ran Jigilar Fasinjoji Fiye Da Miliyan 21 A Yau Ta Jiragen Kasa

October 8, 2025
Kwastam Ta Kama Lita 35,000 Na Man Fetur, Tabar Wiwi Da Sauran Kayayyaki A Kebbi

Kwastam Ta Kama Lita 35,000 Na Man Fetur, Tabar Wiwi Da Sauran Kayayyaki A Kebbi

October 8, 2025
Sin Ta Yi Kira Ga Mambobin WTO Da Su Tinkari Yanayin Tangal-Tangal Tare

Sin Ta Yi Kira Ga Mambobin WTO Da Su Tinkari Yanayin Tangal-Tangal Tare

October 8, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Exit mobile version