Bilkisu Yusuf Ali" />

Gwamna Masari Ya Dawo Da Martabar Jihar Katsina – Bilkisu Qai-qai

Gwamna Masari Ya Dawo Da Martabar Jihar Katsina – Bilkisu Qai-qai

 

HAJIYA BILKISU QAI-QAI na cikin jajirtattun ’yan siyasa mata da su ke bayar da gagarumar gudunmawa a cikin al’umma. ’Yar siyasar ta taka tudu biyu, inda bayan kasancewarta ‘yar siyasa, sannan uwa ce wacce ta kan damu da duk wani hali da mata da yara suka shiga tana iya qoqarinta don ta tabbatar sun sami kuvuta ko waraka. A watannin baya ta sauya sheqa daga jam’iyyar PDP zuwa APC kuma an ganta tana taimakon jam’iyyar APC tamkar ba ta tava zaman PDP ba kuma cikin nasara. Wannan ta sa Wakiliyar LEADERSHIP A YAU, BILKISU YUSUF ALI, ta tattauna da ita, don jin mene ne silar wannan nasarar tata, sannan kuma ya ta ke ganin Katsina da ma qasa bakixaya a yau  a wannan kwanaki 100 a zagaye na biyu na wannan gwamnatin? Ga yadda tattaunawar ta kasance:

 

A da ki na cikin PDP, amma yau ga ki a APC ya ki ka tsinci kanki a hakan?

Ai kin san komai tsari ne na Allah kuma kullum addu’armu Allah ya kai mu kan dai-dai. Sannan burinmu a taimakawa al’ummar Katsina nan ne mahaifarmu nan muka sani kuma ba mu da fin ta don haka muna kallon ina ne inda al’umma za su sami sauqi. Silar nasarata kuwa duk daga Allah ne kuma kin san duk abin da za ka yi zuwa xaya  da iklasi to tabbas zai zame maka alheri. Sannan Maigirma Gwamna Dallatun Katsina mutum ne na kwarai wanda yake kishin qasa tunda kuwa haka ne duk mai son Katsina da kishinta dole ya goya wa Dallatu baya.

 

Ya ‘yan APC su ka karve ki?

Gaskiya ba ni da abin da zan faxa wa jagoran APC maigirma Dallatu Masari da ‘yan jami’iyyar APC gaba xayansu saboda karvana da suka yi hannu bibbiyu suka ba ni dama ba sa bambanta ni da sauran ‘yan jam’iyya sai godiya  Ina APC na shigo APC zan taimakwa jam’iyyar APC jini da tsoka bakin rai bakin fama.

 

Ya ki ke Ganin  Harkar Tsaro a Katsina?

Matsalar  tsaro ai ba iya katsina ba ce, ba ma iya Najeriya ce ba, matsalar tsaro musiba ce da ta addabi duniya.

 

Amma jihar Katsina ce jiharki.

Eh haka ne kuma dai-dai gwargwado nasan abin da yake gudana a Katsina Alhamdlillahi batun harkar tsaro yana nema ma ya zama tarihi don an sami sauqi sosai don maigirma gwamna Rt Honourable Aminu Bello Masari  da kansa ya shiga daji wanda tsakani da Allah mutanen Katsina sun yarda da kwarewa da tausayi irin na Dallatu wanda ya nuna halin halacci ba shugaba ba ne mai kyale talakawansa ba. Mutane sun ga qimarsa da martabarsa da kokarinsa a matsayin shugaba.

 

Amma an ce mai girma gwamna ya rarrashi ’yan ta’adda ne ko?

Ba ya lallashe su ba ne ya faxa musu ya gaya musu cewa ba wanda ya fi qarfin hukuma. Sannan sulhu alheri ne ba a son tashin hankali don haka maigirma gwamna ya faxa musu ba wai rarrashi ba ne na ana jin tsoronsu. Don ba su fi qarfin gwamna ba. In kin lura tunda maigirma gwanma ya je dajin har zuwa yau ba a kai irin wannan hare-haren

 

Ya ki ke kallon tattalin arzikin qasar nan, musamman da ‘yan qasa ke kuka kullum?

Mai girma shugaban qasa kowa yasan mutumin kirki ne duk wani abu da zai yi na al’umma yana yi ne da kyakkyawar manufa. Burinsa farfaxo da tattalin arziqin qasa wanda kuma ga shi nan a fili ana gani. Kalli yadda ya farfaxo da harkar noma da yarda ya dawo da harkar kasuwanci duka da wasu na yi wa abin mummunan fahimta. Fatauci fa asali ya samo tun zamanin Annabi don me Buhari za a ce ya hana? Kawai dai an kasa fahimtar Buhari  ne,  shi burinsa a tsarkake sana’ar a yi mata tsari inda kowa zai amfana  ba yadda za a cutu  ba yadda ba za a ke shigo da miyagun kaya ba, sannan ga  harkar sufuri da sauransu. Ai ko a wajen shigo da kayan maye an sami sauqi sosai ba abin da za mu faxa wa Buhari sai godiya. Tunda duk miyagun ayyuka hatta kidnapping xin nan duk sharrin kwaya ne.

 

To amma a na kukan ya tattare a Kudu su kaxai ke shan romon dimokuraxiya.

Wannan maganganu ne na ‘yan adawa,  amma ko  a arewan ya yi manyan ayyuka kamar yadda ya yi wa kudun kawai idon ‘yan adawa ne ke rufewa amma ya kamata su sani shi fa shugaba Muhammadu Buhari shugaba ne na Najeriya ba shugaban arewa ita kaxai ba sannan muna da yaqinin shugaba ne adali kowa yana da wannan imanin don me to za mu ke kuma shakka? Hatta a wannan zubin na ministoci da manyan muqaman federal kowa yasan Shugaba Buhari ya shirya tsaf don kuma yi wa Arewa ayyukan alheri.  Idan har ba a taimaki arewa ba to ba laifin Buhari ba ne laifin waxanda ya ba wa amana ne.Don Buhari yana iya qoqarinsa. Muna da zavavvun  ‘yan majalisar jiha da na tarayya duk waxannan mataimaka Buhari ne a shiyyoyinsu. Don haka mu tsakaninmu da Buhari sai godiya.

 

Ya  ki ke ganin kwana xarin Dallatun Katsina na komawa kan karagar mulkin jihar Katsina?

Ayyukan maigirma Dallatu qari ne a kan waxanda ya faro daga waccan tenure din duk da babban abin da ya kawo tsaikon wasu ayyukan matsalar tsaron nan ce

 

Wanne fata gare ki ga jam’iyyar APC da Gwamnan Katsina Rt. Hon. Aminu Masari da Shugaban Qasa?

Fatana gare su shi ne fatansu da burinsu na kullum su ga talakawansu suna walwala to ina yi musu addu’ar Allah ya qara riqo da hannunsu Allah ya cika musu burinsu kan Katsina da qasa baki xaya. Jam’iyyar APC jam’iyyar karamci da dattako da sanin ya kamata Allah ya sa ta ci gaba da riqe wannan kambun nata.

Exit mobile version