Connect with us

RIGAR 'YANCI

Gwamna Masari Ya Ja Kunnen Al’ummarsa Kan Bada Mafaka Ga ’Yan Ta’adda

Published

on

A halin da ake ciki kuma gwamnatin Jihar Katsina ta ja kunnen mutanen jihar nan da su guji bada mafaka da ma duk wani nau’in taimako ga ‘yan ta’adda.

Alh. Aminu Bello Masari yayi wannan gargadin ne  wajen bikin cin abincin ranar babbar sallahr wannan shekarar ne. shugaban rundunar sojin sama na kasarn tare da tare da rundunar nan mai lakanin Operation Hadarin Daji da kuma sansanin sojojin dake nan jihar Katsina wanda ya gudanar a filin sauka da tashin jirage na Umaru Musa ‘Yar’adua dake nan jihar Katsina.

Gwamnan ya lura cewa a halin yanzu akwai wasu daga cikin ‘yan ta’adda da suke yo kaura daga cikin dazuzzuka suna sajewa cikin mutane wanda hakan ke zama kafar angulu ga ayyukan jami’an tsaro.

Y bada tabbacin cewa ta hanyar aikin dan sanda tare da jama’a wato “Community Policing” gwamnati zatai duk mai yiyuwa wajen samar da zaman lafiya mai dorewa ga al’ummar jihar nan.

Ta ce ko baya ga yadda jami’an soji ke kara kaimi musamman a yankunan da matsalar taron kamari, suma masarautun jihar nan ba’a barsu a baya ba wajen kokarin lalubo hanyoyin magance matsalolin tsaron.

Gwamnan wanda ya yaba akan yadda jami’an tsaro a wannan jiha suka tasamma yan bindiga haikan yace za’ai kitso ne matsalar ne ba a jihohin Zamfara da Kaduna da Sokoto.

Sai ya bada tabbacin gwamnatin jihar Katsina na bayar da duk wata gudummuwa da zata taimaka wajen kakkabe yan bindigar tare da yaba ma kwazon shugaban kasa Muhammadu Buhari akan nuna damuwarshi akan kalubalen tsaron dake addabar yankin arewa maso yammacin wasar nan.

A nashi jawabin shugaban rundunar sojin sama na kasar nan Air Mershall Sadik Abubakar ya jaddada kudurin rundunar sojin saman na samar da dukkanin kayan aiki da ake bukata ga jami’an sojin saman domin gudanar da aikinsu.

Kamar yadda yace, nan bada jimawa rundunar zata kafa garejin gyaran jiragen sama a jihar.

Yace hakan zai taimaka wajen samun saukin gyaran jiragen a shiyyar rew maso yammacin kasar nan.

Tuni dai an riga an fara share silin da za’ kafa garejin gyaran jiragen saman.

Kazalika ya godema gwamna Masari akan samar da filayen da aka gina sansanonin sojin saman a Katsina da Daura da kuma filin da za’a gina asibitin sojin sama a Daura da kuma filin da aka samar kwanan nan domin gina garejin gyaran jiragen sama.

Tun farko a jawabin shi, shugaban rundunar sojin saman ta musamman Air Mershall Charles Ohowo yace baya ga karfafa kwazon jami’an sojin, wannan taron cin abincin rana da aka shirya tamkar nuna gamsuwa ce ga jami’an sojin saman da suka sadaukar da kawunan su domin ganin anyi maganin kalubalen tsaron day a addabi shiyyar nan.
Advertisement

labarai