Gwamnan jihar Katsina Alhaji Aminu Bello Masari ya umarci ma’aikatar kula da albarkatun ruwa da ya gayyaci wani kamfani na kasar Jamus mai suna K.S.B da su ka kware wajen injinan harba ruwa domin su duba manyan injinan harba ruwa a tashar harba ruwa dake Kofar Kaura da gwamnatin da ta gabata ta samar.
Wannan na da nufin kamfanin ya tantance ko dalilin da ya sanya injinan ba su aiki.
Da ya ke zagayawa da gwamnan a wajen injinan shugaban hukumar samar da ruwan sha na jiha Engineer Babangida Yahaya Abubakar ya ce injinan harba ruwan Dan Kwangilar ya kawo sune kawai amma ba a kafa su ba.
Ya bayyana cewa tsawon lokacin da aka kawo injinan hukumar ta sanyasu kuma sai ta gano basu aiki.
Gwamna Aminu Bello Masari da isarsa ya samu tarba daga kwamishinan kula da albarkatun Alh. Musa Adamu Funtua tare da rakiyar babban sakatare a ma’aikatar Ubale Abdurrahman wanda ya sheda ma gwamnatin irin matsalolin da ake fuskanta na game da rashin ingantaccen amfani da ruwan a fadin jihar wanda injinan suka haifar da dukkanin matsala a fadin jihar Katsina da kewaye.