Sagir Abubakar" />

Gwamna Masari Ya Yi Kira Ga Matasa Da Su Guji Bangar Siyasa

Daga Sagir Abubakar, Katsina

 

Gwamna Aminu Bello Masari ya kara kira ga matasa da su guji bangar siyasa da kuma bin diddikin abinda mutum yake ciki a jihar Katsina.

Gwamnan yayi kirrari a lokacin da ya amshi bakuncin al’ummar katamar hukumar Funtua a karkashin jagorancin mai ba gwamna shawara na musamman akan harkokin majalisa Rabi’u Idris.

Ya bayyana cewa duk wadanda suka bada gudummuwa wajen ruruta wutar bangaran siyasa to wata rana abun su zai dawo mawa.

Haka kuma gwamnan ya jaddada bukatar dake akwai wajen aikata gaskiya da rikon amana a matsayin wata babbar hanya ta cimma nasara a rayuwa.

Alhaji Aminu Bello Masari ya yi nuni da cewa gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari ta fito da tsare-tsare na bunkasa bangaren sufurin jirgin kasa, da bunkasa ayyukan noma domin bunkasa tattalin arzikin al’umma.

Ya bayyana cewa nan bada jimawa bane za a kafa kamfani guida ukku a Funtua domin bunkasa harkokin kasuwanci a yankin.

Tun farko, shugaban tawagar daga karamar hukumar cewa tawagar ta kunshi yan kasuwa da kungiyoyi dabam-dabam.

Kamar yadda ya ce, kungiyoyin suna fadi tashi domin tabbatar da amincewa an aiwatar da shirye-shiryen gwamnati mai ci yanzu.

Sauran wadanda suka yi magana a wajen ziyarar sun hada da Bature Sarkin Awo Usman Usman na kungiyar matasa ta Buhari,  saminu Filin Kwallo, Muhammadu Danal, gwamnati mai ci yanzu a bangaren kiwon lafiya, ilimi, gina hanyoyi da tallafawa matasa daga nan sai shugaban hukumar ilimin bai daya ta jiha Alhaji Lawal Buhari Daura, ya yi kira gay an kwangilar da su ke gudanar da aikin gina magewayi a makarantun firamare da ke jihar nan da su kiyaye da ka’idojin da aka shinfida na kwangilar.

Alhaji Lawal Buhari Daura yayi wannan kiran a wajen wani taro tare da yin kwangila da kuma wadanda suke duba aikin da ya gudana a hukumar.

Ya kuma taya murna ga wadanda suka samu nasarar samun kwangilar da kuma hukumar UNICEF game da tallafin da suke badawa.

A jawabinta, wakiliyar hukumar UNICEF Mrs. Stella Okafus Terbe ta bukaci yan kwangilar dasu kiyaye da wa’adinda aka kyayyade na kammala aikin cikin watanni ukku.

Ta kuma bukaci wadanda suke duba aikin dasu ci gaba da duba aikin yadda ya kamata.

Wani sannane da yake kula da aikin Injiniya Oyama Emanuel ya bayyana cewa ya kamata a gudanar da kwangila dangane da ka’idojin da hukumar UNICEF ta shinfida.

Injiniya Onyama Emanuel ya bayyana cewa magewayin ya sha bamban dangane da na maza da mata domin kare kamuwa daga cututtuka.

Tun farko Daraktan tsare-tsare da kididdiga na hukumar ilimin bai daya Alhaji Isah Musa Kankara ya bayyana cewa hukumar UNICEF da gwamnatin jihar Katsina suke gudanarwa da aikin.

 

Exit mobile version